✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Real Madrid ta casa Celta Vigo a wasan mako na biyu na La Liga

Luka Modric ya sha yabo saboda yadda ya sauya salon wasan.

Real Madrid ta casa Celta Vigo a wasan mako na biyu na gasar La Liga da suka fafata ranar Asabar a filin wasa na Abanca-Balaidos.

Ruwan kwallaye biyar aka yi a wasan da Jesus Gil ya yi alkalancinsa wanda aka tashi 4-1 a gaban ’yan kallo 15,681.

Karim Benzema ne ya fara ci wa Real kwallo a bugun fenariti, sai mai masaukin baki ta farke ta hannun Iago Aspas, shi ma a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Modric ne ya ci wa Real ta biyu daga yadi na 25, bayan da David Alaba ya bashi kwallo.

Daga nan dan wasan Croatia, mai shekara 36 ya bai wa Vinicius Jr kwallo shi kuma ya jefa a ragar Agustin Marchesin.

Federico Valverde ya kara ta hudu a minti na 66.

Real ta kara samun bugun fenariti a karo na biyu, inda Eden Hazard, wanda ya shiga wasan daga baya ya buga amma mai tsaron raga Marchesin ya tare.

Tsohon dan kwallon Chelsea ya ci kwallo hudu a wasa 50 da ya yi wa Real Madrid a La Liga.

Kawo yanzu Real ta yi nasara a dukkan wasa uku da ta fara yi a kakar nan, inda ta doke Eintracht Frankfurt a Uefa Super Cup da Almeria a wasan farko a La Liga.

Modric – wanda magoya bayan Celta suka yi wa tafi ya sha yabo daga bangaren mai horaswar kungiyar, Carlo Ancelottin kan abin da ya kira yadda nuna kwarewa wajen sauya salon wasan.

A yanzu Modric ya ci kwallo a kalla daya a lig a gasar Bosnia da Croatia da England da Sifaniya a kowacce kaka.

Kuma 19 daga kwallo 33 da ya zura a raga a La Liga daga wajen da’ira ta 18 ya ci.

Rabon da Carlo Ancelotti ya yi rashin nasara a wasan La Liga a kan kungiyar da ba daga cikin birnin Madrid ba, tun doke ta Barcelona ta yi a Janairun 2021.