✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar zabaya a Jihar Sakkwato na cike da kalubale

Zabaya wata lalura ce wadda ake gadonta kuma masu ita ke da karancin sinadarin melanin wanda yake taimaka wa fatar jiki da gashi da kuma…

Zabaya wata lalura ce wadda ake gadonta kuma masu ita ke da karancin sinadarin melanin wanda yake taimaka wa fatar jiki da gashi da kuma idanu kamar yadda Kungiyar Zabaya ta Kasa (National Organization for Albinism and Hypopigmentation NOAH) ta bayyana.

Daga cikin irin dimbin matsalolin da zabaya suke fuskanta, kamar yadda Kungiyar NOAH ta bayyana akwai hadarin kamuwa da cutar kansa ta fata musamman a kasashe masu zafi inda zabaya ba sa samun kyakkyawar kulawa, kuma cutar tana haifar wa kwayoyin halittarsu matsaloli ta yadda hakan ke shafar alaka a tsakanin kwakwalwa da idanu.

A’isha Hassan (wadda ake kira da Nasara) wata zabaya mai shekara 50 tana zaune kamar yadda ta saba a wani wuri domin yin bara dab da kofar shiga Hubbaren Shehu Usman Dan Fodiyo a birnin Sakkwato.

A’isha dai makauniya ce wadda suka rabu da mijinta, kuma ita kadai ce zabaya a danginsu gaba daya. Tana yawan zuwa wannan wuri musamman a ranar 27 ga kowane watan Musulunci lokacin da Hubbaren ke tara gomman masu ziyara.

Ranar Alhamis din makon iya ma A’isha ta je wurin kuma tun daga nesa za ka rarrabe tsakaninta da ’yan uwanta mata masu neman sadaka a wurin saboda hasken fatarta. Kuma ta ce tana yin bara ce bisa tilas tun sa’ar da ta rasa mijinta shekara 5 da suka wuce.

Sai dai duk da kalubalen da take fuskanta hakan bai sanyaya mata gwiwa ba. Takan bar gida tun safe tare da ’yarta mai suna Hauwa’u wadda take yi mata jagora duk lokacin da za ta fita. Daga babban titin Ya Katanga da ke Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa, A’isha ke tsallakawa kullum domin isa Hubbare da ke babban Titin Sultan Bello wadda tafiyar mintoci kadan ne a kafa.

Hauwa’u takan koma gida bayan ta raka mahaifiyarta  zuwa Hubbaren, sannan daga bisani ta koma da yamma misalin karfe 4:00 don komawa da ita gida, inda a galibi sukan dada zama har zuwa daukewar sawun masu ziyara da misalin karfe 6:00 na yamma.

A cikin sa’o’i 7 zuwa 9 na ranakun Alhamis da Juma’a da take shafewa a Hubbaren tana bara, A’isha tana samun Naira 300 zuwa 500, amma a wasu lokuta takan samu ninkin hakan, kuma takan samu hatsi da masu ziyara ke kawowa. Da wannan ne take rayuwa a tsawon mako sai kuma wata Alhamis da Juma’a.

Aisha daya ce daga cikin zabayoyin da ke Jihar Sakkwato wadanda Shugaban Gidauniyar Zabaya ta Jihar Sakkwato, Alhaji Abba Galadima Durbawa ya ce suna cikin tsananin ukuba.

Alhaji Abba Galadima Durbawa ya ce,  “Mambobinmu suna cikin kunci saboda suna fama da dimbin matsaloli da suka hada da kalubalen kiwon lafiya da nuna musu kyama da musguna da kuma rashin tallafi daga gwamnati.”

Ya kara da cewa,  kashi 80 cikin 100 na mambobin gidauniyar su 591 da suka fito daga kananan hukumomi 23 na jihar matalauta ne da ba za su iya sayen magani ko ingantaccen abinci ko kariya.

Durbawa ya kara da cewa mutanen da suke fama da lalurar zabaya a jihar ba a ba su aikin gwamnati ko koya musu sana’o’i ko duk wani tallafi na inganta rayuwa na gwamnatin jihar.

“Makarantu suna hana mu guraben karatu,” inji shi. Ya ce duk da cewa wadansu daga cikinsu suna da takardun Ilimi ta Kasa (NCE) da diploma.

“A yanzu gidauniyar ba za ta iya yin komai ba ga mambobinta samad da 500 ba, saboda tana fama da matsalar kudi lamarin da ke sanya mambobinta da suke fama da wasu lalurori na rashin lafiya ba su samun tallafi. Muna da matsaloli da, kamar A’isha a tsakanin mambobinmu, kuma babu abin da za mu iya yi,” inji shi.

Kamar A’isha, Saudatu mai shekara 35 da kanenta Umaru mai shekara 25 su kadai ne masu lalurar zabaya a danginsu.

“Ni da ’yar uwata mu kadai ne zabaya a cikin ’ya’yan babanmu mu sama da 20, kuma an ware mu babu wani tallafi,” inji Umaru wanda yake yawo don neman sadaka.

Yanzu lokacin sanyi, lebbansu kan rika fama da zubar da jini, yayin da jikunansu suke rika yin digon baki sakamakon wasu nau’o’in cututtuka.

Saudatu ta yi aure har sau biyu kuma tana da ’ya’ya hudu daga auren biyu. Biyu daga cikin ’ya’ya biyu daga aurenta na farko suna raye, yayin da biyu na aurenta na baya suka rasu. Ta ce ita take fafutikar kula da ’ya’yanta biyu ba tare da samun tallafi daga ko’ina ba. Tana gudanar da kananan harkokin kasuwanci kamar ‘kwai-da-kwai’(awara). Kuma daga wannan sana’a da ba ta fi jarin Naira 500 ba take kula da ’ya’yanta.

A’isha da Saudatu da Umaru da suke zaune a birnin Sakkwato, amma akasarin zabayan da suke Sakkwato suna zaune a yankunan karkara wadanda suka fi fama da kuncin rayuwa.

An kafa gidauniyar ce don kula da jin dadinsu bayan da aka lura gaba daya ba su da hanyar samun kudi.

A’isha ta ce, “Mijina da ni mun fito ne daga birnin Sakkwato, kuma bayan aurenmu sai muka zauna a ’Yar Katanga kusa da Fadar Sarkin Musulmi da ke kan Titin Sultan inda na ci gaba da rayuwa.”

A’isha ta bayyana yadda a baya ta rika rayuwa kamar kowa ba tare da fuskantar matsalolin da mutanen da aka haifa zabaya suke fuskanta ba.

“Na gudanar da dukan ayyukan gida kamar yadda kowace mace ke yi. Na daka gero don yin fura da nono da kuma daka dawa don yin tuwo. Hatta lokacin da na haihu na yi wanka da ruwan zafi kamar yadda aka saba, kuma fatar jikina ba ta hadu da illa ba. Ba za ka ce ni zabaya b ace in ka ga yadda nake gudanar da harkokin gidan aurena,” inji ta.

A’isha ta haifi ’ya’ya takwas, mata biyar maza uku. Sai dai biyar daga cikinsu sun rasu, inda aka bar ta da ’ya’ya uku, mata biyu namiji daya. Kuma babbar matar aure ce, na biyu namiji ne, yayin da karamarsu Hauwa’u ta kammala sakandare.

Rashin lafiyar A’isha ya faro ne a lokacin da aka gano bushewa da ci a saman lebenta wanda ba ta dauki mataki a kai ba.

“Kasancewar karamin abu ne da zan iya kula da shi, ban je asibiti ba ko in nemi magani, sai na yi watsi da shi. Sannu-sannu sai bushewar da cin ta karu ta ci gaba da girma har ta cinye min leben sama gaba daya,” inji ta.

Ta kara da cewa; “Cutar ta ci gaba da cinye mata fuska, inda ta bata mafi yawan hancinta ya yi kofar da ta jawo mata wahala a rayuwa. Daga baya sai aka tura ni Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo (UDUTH) inda aka yanki fata aka cike gibin da ke cikin bakina. Yanzu maganar nan ban iya jin ki yadda ya kamata, kuma na rasa idona,” inji ta.

A Asibitin UDUTH a shekarar 2014, an yi mata gwaji aka gano tana da cutar sankarar fata. Sankarar ta lalata wasu sassa na fuskarta, kuma an samu nasarar yi mata aiki na farko.

Wani likita a Asibitin UDUTH Dokta Bashir ya ce tilas ne a kan masu jinya su rika dawowa ana duba su, amma A’isha Hassan ta gaza yin haka saboda rashin kudi.

“Matsalar Sankarar ta dawo daga baya aka sake turo ta wurinmu don yi mata aiki karo na biyu, ta zo nan a ranar 24 ga Disamban bara, amma zuwa Fabrairun bana sai ta daina zuwa, ba mu san me ya sa ta yi watsi da jinyar ba,” inji shi.

Sai dai ya ce, nau’in jinyar sankarar ta danganta ce da irin halin da mutum yake ciki, kuma za a iya magance matsalar A’isha in aka tsaya.

Hauwa’u ’yar Aisha ta damu sosai lokacin da ta ga mahaifiyarta ta shiga wannan mugun hali.

“Ba mu da masu kudi a danginmu, dukan ’yan uwanmu ya alla bangaren miji ko dangin mahaifina talakawa ne irinmu kuma babu wanda yake da niyyar ya taimaka mana,” inji Hauwa’u.

Gidauniyar Zabaya da ke Sakkwato ta ce ta dan yi abin da za ta iya wajen tura matsalar Nasara (wata zabaya) zuwa ga Majalisar Sarkin Musulmi wadda ta dauki nauyin yi mata jinya a lokuta biyar daban-daban a Asibitin UDUTH.

Kuma kasancewar Gidauniyar Zabaya tana da rajista da Ma’aikatar Bunkasa Jin Dadin Mata da Wasanni ne, Aminiya ta ziyarci ma’aikatar inda Babban Sakataren Ma’aikatar Alhaji Ladan ya bayar da tabbacin cewa za a kula da jin dadin zabayan.

Ya yi alkawarin cewa ma’aikatar za ta tattauna da shugaban gidauniyar kan halin da suke ciki don samar da mafita tare da mika batun zuwa ga Ma’auikatar Jin Dadin Jama’a da ta Harkokin Addini don su ci gajiyar wasu ayyukan kyautata rayuwar jama’a na gwamnatin jihar.