Sami Yusuf, fitaccen mawakin Musulunci ne. Asalinsa dan kasar Iran ne amma yana zaune a Birtaniya. An haife shi a watan Yuli na shekarar 1980.
Ta fuskar waka kuwa, shi dan gado ne, domin kuwa iyayensa, ’yan kabilar Azeri, mawaka ne da suka shahara. Wannan ta sanya waka ta zama wani bangare na rayuwarsa tun yana dan yaro.
Tun farko dai mahaifinsa ne ya fara dora shi kan harkar waka, domin shi ya fara koya masa sana’ar tun yana dan karami. Mahaifin nasa ya yi fice wajen rubutawa da kuma rera wakoki.
Kamar yadda Aminiya ta kalato, shi dai Sami, ya tashi ne a birnin Landan, inda ya koyi sarrafa na’urorin kade-kade da bushe-bushe na zamani, inda daga bisani kuma ya kara shakuwa da maida hankali don ganin cewa ya kware a fagen rubutawa da harhada waka, ta yin amfani da hikimomi da dabarun zamani.
Ba haka ya tsaya ba, sai da ya shiga makarantu daban-daban na koya sana’ar kida da waka. Ya taba daukar darussan waka a babbar makarantar nan ta mawaka da ke Landan, wato Royal Acadamy of Music.
Kasancewar tun yana karamin yaro ya fara wannan sana’a ta waka, gami kuma da baiwar daddadar murya da Allah Ya ba shi, ya samu amsuwa a duniyar mawaka cikin kankanen lokaci. Baya ga wannan, Sami ya lakanci al’adu da al’amuran nishadantarwa irin na al’ummar Gabas Ta Tsakiya da kuma na Turawa.
Kamar yadda wani mai sharhi kan wakoki, wanda kuma ya dade da sanin Sami ya fada, ya ce: “Hakika, yana da wahala ka samu mawakin da ya tattara hazaka da fasaha irin na Sami. Ya kasance cikakken Musulmi mai kishin addinisa, wanda kuma yake zaune a kasar Turai. Shi mutum ne da ya yi amannna da cewa, ta hanyar wakoki, zai iya daukaka darajar addininsa na Musulunci. A mafi yawan wakokinsa, yakan yi kokarin jan hankalin matasa da cewa su rika yin alfahari da addininsu na Musulunci.”
A cikin shekarar 2003, Sami ya fitar da faifan wakokinsa mai suna ‘Al-Mu’allim’ da kuma faifansa na biyu wanda ya yi wa taken ‘My Ummah’ (Al’ummata). Wadannan faya-fayan, sun yi tashe sosai, inda aka samu rahoton cewa an sayar da kwafi miliyan biyar na wakokin a duk duniya.
Yakan yawata duniya domin gabatar da wakokinsa, musamman ma yakan ziyarci kasashen Nahiyar Turai da Gabas Ta Tsakiya da kuma Amurka, inda yake da masoyan wakokinsa da dama. A kasar Turkiyya kuwa, yana da masoya kimanin 250, 000.
Saboda irin daukakar da Allah Ya yi masa ta fuskar sana’arsa ta waka, shararriyar mujallar nan ta duniya, Time Magazine ta taba tattaunawa da shi, kuma ta ba shi wuri na musamman. Haka ma, ya sha bayyana a cikin mujallu daban-daban, a sassan duniya daban-daban.
Mafi yawa da jigogin wakokinsa sun ta’allaka ne wajen jaddada sakonnin soyayya, jinkai, zaman lafiya da kuma hakuri, kamar kuma yadda yake yada addinin Musulunci ta fuskoki da dama.
Rayuwar mawakin Musulunci Sami Yusuf
Sami Yusuf, fitaccen mawakin Musulunci ne. Asalinsa dan kasar Iran ne amma yana zaune a Birtaniya. An haife shi a watan Yuli na shekarar 1980.Ta…