✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar Matasa a Dandalin Abota na Intanet (2)(3)

Samuwa da yaduwa da bunkasar dandalin abota a Intanet ya kashe wa zauruka da majalisun tattaunawa kasuwa, duk da cewa har yanzu akwai su.  Dalilan…

Samuwa da yaduwa da bunkasar dandalin abota a Intanet ya kashe wa zauruka da majalisun tattaunawa kasuwa, duk da cewa har yanzu akwai su.  Dalilan bunkasa da habakarsu kuwa ba nesa suke ba.  
Abu na farko, shi ne, ingantuwar hanyoyin gina manhajar sadarwa tsakanin gidan yanar sadarwa zuwa wani gidan.  Sai yaduwar na’urorin sadarwa masu dauke da ka’idar sadarwar Intanet (Internet Protocols) irin su wayoyin salula da dukkan nau’ukansu (kamar su iPhone da iPad da iPod da BlackBerry da Samsung Galady Note da sauransu).  Abu na uku, shi ne, saukin hanyoyin rajista a wadannan dandalin abota.  
A yayin da ake bukatar dole sai ka kai shekara 18 kafin ka iya mallakar akwatin I-mel, a wajen rajistar mallakar shafi a dandalin abota ana bukatar shekara 13 ne kacal.  Abu na hudu, shi ne, bunkasar hanyoyin kasuwanci da nau’ukansu a giza-gizan sadarwa na Intanet. Abu na biyar, shi ne, saukin mu’amala da wadannan shafuka suke tattare da shi.  Duk rashin karatunka kana iya sarrafa su iya gwargwado.  Sai abu na shida, wato ingantuwar tsarin sadarwar fasahar Intanet a kasashe masu tasowa, musamman Nahiyar Afirka da Gabas-ta-Tsakiya da Gabashin Asiya da kuma Kudancin Amurka.
Wannan bunkasa tana da ban al’ajabi matuka.  Domin ba matasa kadai ya game ba, har da manya da tsofaffi da kuma kananan yara.  Ba ’yan birni kadai abin ya shafa ba, har da ’yan karkara da makiyaya. Kai, lamarin ma ya hada da nakasassu ta bangaren gani da ji; duk ba a bar su a baya ba. Shahararru daga cikin dandalin abota da aka fi shawagi a cikinsu su ne: Dandalin Facebook da Dandalin Twitter da Dandalin Instagram da Dandalin Pinterest, da kuma Dandalin Google+.  Wadannan dandamalai dai ana ji da su a kasashen duniya, saboda tasirinsu wajen kame zukatan masu mu’amala da su. Abin ya wuce hankali da sanin ya kamata.
Dandalin Facebook, wanda ya faro daga dalibar jami’a zuwa ’yan sakandare shekara 8 da suka gabata, a yanzu yana da mambobi masu rajista a duniya sama da biliyan daya da miliyan 200!   Mutum miliyan hudu ne suka “so” jawabin nasara da Shugaba Obama ya rubuta a shafinsa na Facebook. Kashi 25 cikin 100 masu amfani da shafin Facebook ba su damu da wata kariya ba. A duk wata akalla mutum miliyan 800 ne ke shiga Dandalin Facebook. Mutum miliyan 488 ne kuma ke mu’amala da shafin Facebook ta wayar salula. Sama da kashi 23 cikin 100 kan shiga shafinsu na Facebook sau biyar a duk yini.  Akalla akan shigar da hotuna sama da miliyan 250 a duk rana. Zuwa karshen shekarar 2012, an saurari wakokin da tazarar lokacinsu ya kai tsawon shekara dubu 210, a Dandalin Facebook. Kashi 80 cikin 100 na masu neman hajojin kasuwanci sun fi son samunsu ta hanyar Dandalin Facebook. Kashi 43 cikin masu mu’amala da shafukan Facebook maza ne, a yayin da sauran kashi 57 cikin 100 din duk mata ne .
A bangaren Dandalin Twitter ma haka lamarin yake.  A tsawon kwanakin shekarar 2012, duk rana masu mu’amala da Dandalin Twitter kan aika sakonni miliyan 175.  Ya zuwa yanzu bayan bude shafin Twitter, an samu sakonni sama da biliyan 163. Jawabin nasarar Shugaba Obama ne ya fi kowane sako yawan tallatawa, yayin da aka tallata shi (retweeted) sau miliyan 800!  Lokacin zaben kasar Amurka da ya gabata an aika da sakonnin da suka danganci zabe wajen biliyan 31 da miliyan 700!  Cikin masu amfani da fasahar Intanet gaba daya, kashi 32 cikin 100 na amfani da masarrafar Twitter. A tsawon kwanakin shekarar 2012, a duk rana an samu masu rajista akalla miliyan daya.  Shafin da jama’a suka fi bi a Dandalin Twitter, shi ne, na shahararriyar mawakiya Lady Gaga, inda ta wayi gari da masu bin ta sama da miliyan 31. Shafin kamfanin da jama’a suka fi bi a dandalin twitter, kuma shi ne, na Youtube, inda ya samu masu bi sama da miliyan 19.  Kashi 50 cikin 100 na masu mu’amala da Dandalin Twitter na yin haka ne ta hanyar wayar salula. Kai jama’a, in takaice muku labari, a Dandalin Twitter a duk sakwan guda, sai an samu masu rajista mutum 11.
Idan muka koma bangaren Dandalin Google+, wanda bai jima da bayyana ba, za mu ga abin mamaki nan ma. Shafin, wanda gwarazan masana harkar manhajar kwamfuta sama da 500 ne suka gina shi, ya zuki Dala na gugar Dala wajen miliyan 585!  A duk rana jama’a kan matsa alamar Google+1 sau biliyan 5!  Cikin kashi 100 na kamfanonin da suka fi yawan dukiya a duniya, kashi 48 cikin 100 na da shafi a Dandalin Google+.  A duk rana mutane sama da dubu 625  ne ke amfani da shafin Google+.  Cikin mutum miliyan 400 da suka mallaki shafi a Dandalin Google+, kashi 27 ne masu aure, sauran duk  tuzurai ne; marasa aure.  Cikin wannan adadi har wa yau, kashi 68 cikin 100 maza ne, sauran kashi 32 cikin 100 mata ne.  Kashi 60 cikin 100 na mamabobin Dandalin Google+ kan shiga shafinsu a duk yini .
Wannan kididdiga mai kama da almara, kadan ce daga cikin abubuwan mamaki da wadannan shafukan abota suke dauke da su.  Goma daga cikin mafiya yawansu su ne: Facebook (biliyan 1 da miliyan 200), sai Twitter (miliyan 500), sai kzone (miliyan 480), sai Google+ (miliyan 400), sai kuma SinaWeibo (miliyan 300).  Sauran sun hada da: LinkedIn (miliyan 160) da Orkut (miliyan 100) da NetLog (miliyan 95) da hi5 (miliyan 80), sai kuma dandalin MySpace, wanda tuni ya mace (miliyan 30) .