✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar mai bin Yesu Kiristi a yau da kullum (2)

Ku yi kaunar magabtanku: “Kun ji an fadi, ka yi kaunar makwabcinka, ka ki magabcinka: amma ni ina ce muku, Ku yi kaunar magabtanku, kuma wadanda…

Ku yi kaunar magabtanku:
 “Kun ji an fadi, ka yi kaunar makwabcinka, ka ki magabcinka: amma ni ina ce muku, Ku yi kaunar magabtanku, kuma wadanda sukan tsananta muku, ku yi masu addu’a; domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin Sama: gama Yakan sa rana taSa ta fito wa miyagu da nagargaru, Yakan aiko da ruwa bisa masu adalci da marasa adalci. Gama idan kuna kaunar wadanda ke kaunarku, wace lada ke gare ku? Ko masu karbar haraji ba haka suke yi ba? Idan kuwa kuna gaida ’yan uwanku kadai, ina kun fi wadansu? Ko al’ummai ba haka suke yi ba? Ku fa za ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama cikakke ne.”(Matta:5:43–48); “ Kada ku zama mabaratan komai ga kowa, sai dai na kaunar juna, gama wanda ya kaunaci makwabcinsa ya cika shari’a. Gama wannan ba za ka yi zina ba, Ba za ka yi kisan kai ba, Ba za ka yi sata ba, Ba za ka yi kyashi ba, kuma idan da wata doka, an turke ta cikin wannan magana, cewa, sai ka yi kaunar makwabcinka kamar ranka. kauna ba ta aika mugunta ga makwabcinta ba; kauna fa cikar shari’a ce.” (Romawa:13:8–10).
Maganar Allah tana cewa; “Kun ji an fadi, ka yi kaunar makwabcinka, ka ki magabcinka.” Irin wannan rayuwa, ita ce ta fi sauki a cikin duniya; amma kafin mu ci gaba, ina so mu gane wane ne makwabci; kuma wane ne magabci; idan har mun gane ma’anar wadannan kalmomin sosai, za mu fahimci koyarwar Yesu ga almajiransa, wato wadanda suka rigaya suka ba da gaskiya gare shi. Tambaya ta farko ita ce; wane ne makwabcina? Akwai wanda ya yi irin wannan tambaya a cikin Littafi Mai tsarki, bari mu duba tare daga cikin Luka:10: 27–37: “Ya amsa ya ce, sai ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da dukan karfinka da dukan azancinka da makwabcinka kuma kamar ranka. Ya ce masa, ka amsa daidai: ka aika wannan za ka yi rai. Amma shi, domin yana so ya baratar da kansa ya ce wa Yesu, WANE NE MAkWABCINA? Yesu ya amsa ya ce, Wani mutum yana tafiya daga Urushalima zuwa Jerico; ya gamu da mafasa, suka yi masa tsiraici, suka doddoke shi, suka tashi, suka bar shi tsakanin rai da mutuwa. Wani Malami yana bin wannan hanya: sa’adda ya gan shi, ya raba ta wancan gefe, ya wuce. Haka kuma wani Lawi, sa’adda ya zo wurin, ya gan shi, shi ma ya raba ta wancan gefe, ya wuce. Amma wani Ba-samariye yana cikin tafiya, ya kawo wurin da yake: sa’ad da ya gan shi, ya yi juyayi, ya zo wurinsa, ya daure raunukansa, yana zuba masu mai da ruwan inabi; ya hawar da shi bisa dabbarsa, ya zo da shi wani mashidi, ya yi dawainiya da shi. Washegari kuma ya fita da sule biyu, ya ba Ubangijin mashidi, ya ce, ka yi dawainiya da shi; abin da za ka batar gaba da wannan, sa’ad da na komo, na mayar maka. A cikin wadannan uku fa, wa ka zata ya zama makwabci ga wanda ya gamu da mafasa? Ya ce, wannan da ya nuna masa jinkai, Yesu ya ce masa, je ka, ka yi haka nan.”
Ba abu mai wuya ba ne mutum ya kaunaci abokinsa, ko na kusa da shi. Wannan kowa zai iya yi a sauwake. Damuwar takan zo ne lokacin da aka ce ga wanda yake gaba da kai, kuma ka sani; sai a ce da kai ka kaunaci irin wannan – gaskiyar shi ne bai da sauki ko kadan. Mutanen duniya sukan kara da cewa, ka so mai sonka ka kuma ki mai kinka, idan har wani ya san cewa mutum yana shirya masa makarkashiya; yana so ya yi masa rauni, abin da ya kamata ya yi bisa tunanin mutum, shi ne ya rabu da wannan mutum. Wani lokaci ko gaisuwa ma babu tsakaninsu: kuma a cikin tunani na ’yan Adam, babu laifi ko kadan cikin irin wannan halin. Amma ga mai ba da gaskiya ga Yesu Kiristi, koda yake mai yiwuwa muna da cikakken hujja mu yi kamar sauran mutane, ba za mu iya yin haka ba tare da saba wa koyawar Ubangijinmu Yesu Kiristi ba. Masu bi a yau suna fuskantar tsanani sosai ta fannoni daban-daban; watakila kana zama da wanda ba ya so ya gan ka da rai, mai yiwuwa har da iyalinka duka, ba abin mamaki ba ne kuma a yanzu; mun ga makwabta da suka hada baki da wadansu suka zo suka yi wa iyalan masu bin Yesu Kiristi yankan rago a gidansu. Wani lokaci ba kisa ba ne amma nuna bambanci a wurin aiki, mai yiwuwa ka yi yi karatu ka kuma kware a fannin karatunka, amma idan lokaci ya yi da ya kamata ka yi shugabancin wannan sashi, sai ka ga an dauko wanda kai ka koyar da shi a ba shi wancan mukami; a dora shi bisanka kawai domin addini – kai Kirista ne; an so ka dauki umarni daga wanda kai ka san cewa dalibinka ne; ba abu ne mai sauki ba ko kadan. Muna gani yau da kullum yana faruwa. A cikin irin wannan yanayi; mene ne ya kamata masu bin Yesu Kiristi su yi? Ubangijinmu Yesu Kiristi da kansa ya ba da asirin tafiya da irin wadannan mutane. A cikin koyarwarsa na Littafin Matta:5:44, Yesu Kiristi ya ce “Amma ni ina ce muku, ku yi kaunar magabtanku, kuma wadanda suka tsananta muku, ku yi musu addu’a.”  Duk lokacin da ka fuskanci damuwa irin wannan; ka tuna da wannan koyarwar, asirin cin nasara bisa kowane magabci shi – nuna masa sahihiyar kauna da kuma yin addu’a dominsa. Addu’a; ba domin su mutu ba kamar yadda na sani wadansu mutane ke yi, amma domin su samu alherin Allah; kada mu yi kuskuren la’antar wani domin muna ganin ya yi mana ba daidai ba. Makaman yakin mu masu bi su ne – kAUNA da ADDU’A, zai zama kuskure ga kowane mai bin Yesu Kiristi ya dauki wadansu irin makamai. Bindiga, ko adda, ko wuka da makamantansu, ba kayan fadan masu bi ba ne, yakin kowane cikakken mai bi a kan gwiwarsa yake yi cikin addu’a a gaban Allah Masanin komai duka. Lallai babu shakka zai zama da wahala ga wanda ba shi da Ruhun Allah a cikinsa, ga mai bin Yesu Kiristi wannan ita ce asirin cin nasara bisa kowane mutum mai gaba da kai a kowane fanni. Akwai dalilin da Yesu Kiristi ya koyar da almajiransa haka , ya ce “Domin ku zama ’ya’yan Ubanku Wanda ke cikin sama: gama Yakan sa ranataSa ta fito wa miyagu da nagargaru, Yakan aiko da ruwa bisa masu adalci da marasa adalci.” Idan har muna so mu bi gurbin Ubangijinmu Yesu Kiristi, babu wata hanya da za mu bi sai wannan da ya koya mana. A cikin rayuwar yau da kullum, sai mu tuna cewa mu ne hasken wannan duniya, bari mu bar wannan hasken ya haskaka. Ubangiji Ya taimake mu iya tafiya da ta cancanci kiranmu.
Kada mu manta da yin addu’a domin zaman lafiya a kasarmu. Ubangiji Allah Ya tsare mu duka, amin.