✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rayuwar Dabbobi: ’Ya’yan kwadi na kamanceceniya da ’ya’yan kifi

Akwai nau’ikan kwadi 6,000 a duniya.

Kwadi dabbobi ne masu rayuwa a cikin ruwa ko a tudu. Ana samunsu a ko’ina, gida ko daji.

Akwai ire-iren kwadi da daman gaske, ciki har da masu dauke da dafin da ke da karfin hallaka mutum da sauran dabbobi muddin aka ci.

Suna daga cikin dabbobi masu kakkarfan kafafu wanda kan ba su damar tsallake duk wata cutarwa da ta tunkaro su.

Wadannan gabbai masu kwarin, su ne sirrin nasarorin da kwadi kan samu saboda da su ne suke iya yawon neman abinci, kuma da taimakonsu suke guje wa duk wata cutarwa.

Dangane da rayuwar kwadi, akan samu canje-canje da dama da kan auku tun daga zuba kwai zuwa kyankyashewa, zuwa kuma lokacin da ‘ya’yan za su yi girma.

Rayuwar Kwadi a takaice

Rayuwar kwado na farawa ne daga lokacin da uwar ta zuba kwai. Suna zuba daruruwan kwai a lokaci guda musamman a kan ruwa, kamar bakin rafi ko gulbi da makamantansu.

Sun fi zuba kwai a lokacin bazara, gab da lokacin da ke sa ran saukar damina. Kwan kwadi a cure suke kuma manne da juna kamar igiya.

Kwan kwadi kan dauki mako daya zuwa uku kafin kyankyashewa.

Sabbin kyankyasar ’ya’yan kwadi na kama da ’ya’yan kifi matuka. Idan ba a kula da kyau ba, za a iya daukar ‘ya’yan kwadi a matsayin kifi idan suna ‘yan kuci-kuci.

Yayin da girmansu ke karuwa, haka kamanninsu zai ci gaba da sauyawa har zuwa lokacin da halittar jikinsu za ta cika.

A makon farko zuwa na biyu da kyankyashewa, ‘ya’yan ba su shawagi nesa daga inda suka kyankyashe, saboda amfanin da sukan samu daga tarkacen kwan bayan kyankyasa.

Sabanin manyan, ‘ya’yan kwadin da ba a jima da kyankyashewa ba ba su iya barin ruwa zuwa tudu don neman abinci, don haka za su ci gaba da zama a cikin ruwa suna kalatar abin da ya sawaka suna ci.

Bayan makonni 14 da kyankyasa, a lokacin kuma girma ya zo har da kafafuwa, yanzu halin yawatawa zuwa neman abinci ya samu, walau a cikin ruwa, ko a tudu.

Da farko, kafafun baya ne ke soma fitowa kafin na gaba, kana daga bisani jikinsu ya shiga canza kamanni zuwa na asalin kwado da aka sani.

Masana sun ce, matakan sauyi na rayuwar kwadi kan auku da sauri idan ya zamana an kyankyashe ‘ya’yan a ruwan da ke da manyan kifayen da ka iya takura musu.

A nan, ‘ya’yan za su yi saurin girma sannan su tsere su bar wurin don tsira da ransu daga farmakin manyan kifayen.

Idan kuwa ya zamana babu wata takura a ruwan, matakan sauyin kan yi jinkiri wajen aukuwa, sannan za su iya zama mai tsawo a wurin, kamar shekara ko makamancin haka.

Masana kimiyyar dabbobi sun ce, kwado na iya rayuwa na tsawon shekara 20 muddin aka kebe shi ana ba shi kulawa.

Akwai nau’ikan kwadi 6,000 a duniya

Sannan ana da nau’ikan kwadi da yawansu ya kai 6,000 a fadin duniya, kuma har yanzu ana kan gudanar da bincike don gano wasu sabbi.

A baya-bayan nan, masana kimiyya a kasar Ecuador sun gano wasu sabbin nau’in kwadi a gabashin kasar, inda suka bukaci a sanya su cikin jerin dabbobin da ke fuskantar barazanar bacewa a doron duniya.

Bayanai sun nuna Colombia da Ecuador na daga jerin kasashen da suka fi yawan kwadi a duniya, wanda kwararru ke tunanin akwai sabbin nau’ukan da kawo yanzu ba a iya gano su ba.

Masanan sun gano cewa, kwadon nan mai suna ‘Goliath’ wanda ba a samun shi a ko’ina in banda Afirka ta Yamma, shi ne kwado mafi girma a duniya wanda tsayinsa ya kai inci 15.