Ruwan ambaliya ya mamaye al’ummomi sama da 60 a yankin Ƙaramar Hukumar Abaji da ke Jihar Kogi.
Shugabar ƙungiyar al’ummar yankin, Farfasa Joy Ede Ukoje, ta bayyana bukatar kai musu ɗauki da kayan agaji domin rage raɗaɗin asarar da ambaliyar ta haifar.
Ta bayyana a ranar Alhamis cewa halin da jama’a ke ciki a yankuna irin Abaji, waɗanda ke kusa da ruwa, ya fi ƙarfin gwamnatin jihar kaɗai.
Don haka ta roki hukumomi da ɗaiɗaikun mutane da kungiyoyi su taimaka wa yankunan da abin ya shafa.
Farfesa Joy ta ce, “a cikin ƙananan hukumomi tara da ake yawan samun ambaliya a jihar Kogi, a kodayaushe na Abaji ya fi muni, kusan duk al’ummomin yankin ne suke rasa muhallansu da hanyoyin dogaro da kansu.”
Ta ce kungiyar al’ummar yankin na kokarin tallafa wa waɗanda abin ya shafa, amma ya kara da rokon gwamnatin tarayya da jihar da na ƙasashen duniya da ɗaiɗaikun mutane su kawo musu ɗauki