✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Rayuwar Dabbobi: Shin me ya sa kyanwa ke binne kashinta?

Kyanwa na da dabi'ar son jiki, shi ya sa wasu lokuta sukan kwanta da mutane a shimfida daya.

Kyanwa na daga cikin nau’in dabbobin da mutane kan ajiye su kiwata a gidajensu, kuma akan same su a gida da daji.

Yayin da wasu kan kiwata kyanwa domin sha’awa, ko samun abokin zama don debe kewa, wasu kuwa kan kiwata su ne domin korar wasu halittun da suka addabi mutane a gida, kamar beraye, kadangaru da makamantansu.

Suna daga dangin dabbobin da ke da dabi’ar shayayarwa – wato sukan shayar da ‘ya’yansu bayan haihuwa.

Haka nan dabba ce mai cin wasu dabbobi a matsayin abinci. Alal misa, Kyanwa na cin bera da kadangare da kifi da ‘yan tsaki da sauransu.

A wasu lokutan har ciyawa kyanwa na ci, lamarin da wasu masana ke cewa hakan na fruwa ne sakamakon wasu muhimman sinadarai da ciyawa ke dauke da su kuma masu amfanin ga lafiyarsu.

Yadda kyanwa ke haihuwa

Dauka da renon ciki har zuwa haihuwa ga kyanwa, yana kai tsakanin kwanaki 64 zuwa 67. Sannan takan haifi ‘ya’ya da dama a lokaci guda, kama daga biyu, uku, hudu zuwa abin da ya sawwaka.

Kididdiga ta nuna cewa, 127 daga cikin ‘ya’yan kyanwa 169 ke mutuwa kafin su cika wata shida da haihuwa saboda farmakin karnuka da sauran hadurran da sukan fuskanta.

Kaifin Gani

Duk da dai kyanwa na zirga-zirga kowane lokaci, sai dai masana sun ce zirga-zirgar ta su ta fi karfi a lokutan dare.

Idanun kyanwa na da kaifin gani musamman da daddare, sannan suna da baiwar jin sautin motsi daga nesa wanda albarkacin hakan suke iya bibiyar kananan kwari ko dabbobin da suke kamawa suna ci.

Kyanwa kan shafe tsawon lokaci tana barci

Yawan barci na da matukar muhimmanci a rayuwar kyanwa, saboda haka na kara musu lafiya da karfin jiki, musamman ma a lokutan da girma ya fara cim musu.

Kyanwa kan yi barci akalla na sa’o’i 12 zuwa 16 duk yini, wasunsu ma kan rufa sa’o’i 20.

Yadda kyanwa ke aika sako

Kamar sauran halittu, kyanwa suna da hanyoyin da suke amfani da su wajen sadarwa a tsakaninsu don isar da sakonni, daga ciki akwai kukan nan da aka sansu da shi, wato “Miyawn” da sauransu.

Fushin kyanwa

Kyanwa na da fada musamman idan tura ta kai mata bango. Sai dai mazan sun fi fada. Takara kan mace yayin neman saduwa da ita na daga cikin manyan dalilin da ke haifar da fada a tsakanin kyanwa.

Yayin da macen kyanwa ta fi nuna fushinta a lokacin da aka kusanci ‘ya’yanta sa’ilin da take cikin danyen jego.

Kyanwa uwar son jiki

Suna da dabi’ar son jiki, shi ya sa wasu lokuta sukan kwanta da mutane a shimfida daya.

Wasu kyanwa kan rikide su gawurta, su addabi mutane da sace-sace a gida da unguwa.

Sabo turken wawa

A cewar masana, saboda fikira irin ta kyanwa, ya sa ko da an raba ta da asalin gidan da take zuwa wani gida mai nisa, muddin ba rufe mata idanu ba a lokacin da aka dauke ta din, za ta iya komawa inda aka dauko ta ba tare da jagora ba.

Ko me ya sa kyanwa kan turbude abin da suka ci ya rage da kuma kashinsu a kasa?

A cewar masana rayuwar dabbobi, sukan yi hakan ne domin kare kansu daga sharrin manyan dabbobi na gaba da su, kamar kare da sauransu.