Zaki sarkin dawa, in ji masu azancin magana.
Ga shi dai ba shi ne mafi girman kwaron dawa ba, amma shi ake yi wa lakabi da sarki saboda kwarjininsa.
Galibin zakoki ana samun su ne a yankin Afirka, sai kuma kalilan a wasu sassan duniya, kamar Indiya da sauransu.
Nauyin rikakken zaki na kai kilogram 190, macen kuwa kilogram 126.
Nauyi da kuma karfin da suke da su na matukar taimaka musu wajen farautar manyan kwarin dawa da kuma iya kare kansu daga cutarwar takwarorinsu.
Gashin wuya da ake ganin zaki da shi wata kwalliya ce da ke kara masa kwarjini.
Idan rikakken zaki ne, tsayin gashin na kaiwa senimia 16.
Kazalika, gashin addo ne na musamman da sukan burge matansu da shi, kuma yakan kare su daga jin rauni a wuya da kai yayin fada.
Matan kan hada kai wajen rainon ’ya’yansu.
Muddin a cikin ahali guda ne, kwikuyon zaki na iya shan nonon kowacce daga cikin iyayensu ko da ba ita ce ta haife shi.
Ita kuwa uwar ba za ta kyamaci dan ba duk da asali ba ita ce ta haife shi ba, irin halin da ba safai akan samu a sauran dabbobi ba.
Aikin mazan ne bai wa ahalin kariya daga barazanar sauran mayan namun daji a kowane lokaci.
Zakoki na da juriya, domin kuwa suna iya rayuwa a wurare da ake da karancin ruwa kamar sahara da sauransu.
Zaki dabba ce mai ci da yawa. A tashi daya yana iya cin naman da ya kai kilogram 40, kwatankwacin kashi daya bisa uku na jikinsa.
Duk da dai zaki na yin farauta a kowane lokaci, sai dai farautar dare ta fi masa armashi saboda yanayin kaifin ganinsa a cikin duhu.
Suna matukar jin dadin yin farauta a lokacin da ake hadari da iska mai kura, saboda hakan kan hana abin farautarsu ganin wuri da kyau da kuma jin motsi yadda ya kamata.
Galibi, zuwa farauta nauyi ne da ya rataya a kan matan, su ke zuwa su farauto abin da za su ci da ahalinsu.
Gurnanin zaki na da karfi kuma yana tafiya da nisa; masana sun ce ana iya jin gurnanin zaki daga nisan mil biyar.
A cewar masana, a halin da ake ciki, adadin zakokin da suka rage a fadin duniya ba su wuce 23,000 wanda hakan ke nufin kashi 10 cikin 100 ne kawai suka rage a raye.
Bincike masana ya nuna abin da ya karar da zakoki har da yawan kashe su da akan yi don kare rayuka da dabbobin jama’a, musamma a karkara.
Haka nan, sauyin yanayi na daga dalilan da suka haifar da karancin zakoki a dazuzzukan duniya.
Sai kuma mafarautan da kan kashe su ba bisa ka’ida ba don safarar sassan jikinsu.