Gizo-gizo kwaro ne da ake da ake iya gani a ko’ina, gida ko daji kuma nau’ika da sifofi daban-daban, manyan da kanana.
Masana sun ce awkai nau’ikan gizogizo akalla 35,000 da aka sani a doron kasa, sannan akwai da yawan gaske wadanda ba a kai ga ganowa ba.
- Kyankyaso: Kwaron da ke iya rayuwa tsawon mako daya babu kai
- Karshen fadan Kumurci da Mesa, mutuwar kasko
Sun ce dafin gizogizo na iya yin ajalin mutum saboda kaifinsa, amma kuma ba duka gizo-gizo ke da dafi ba, don haka ba kowanne ne cizonsa ke da illa ba.
Binciken masana ya nuna macen gizogizo na da cin tsiya, wanda hakan ya sa wasu lokuta idan wuri ya yi wuri, matan kan kama mazan su yi kalace da su.
Sai dai wannan dabi’ar ta kebanta ne kawai da wasu nau’ikan na gizogizo.
Game da sakar gizogizo kuwa, a ido tamkar abu ne mara kwari, amma a hakikanin gaskiya sakar gizogizo na da kwari gwargwado, in ji masana.
Kwarin sakar ne ya sa wasu lokuta ba kananan kwari kadai ba, har da manyan tsuntsaye suna iya makalewa cikin sakar gizogizo su kuma zama abin kalacensu.
Ruwan jikinsu wanda ke mazaunin jini, launin shudi gare shi, sabanin na sauran kwari.
A cewar masana, namijin gizogizo na da dabi’ar yi wa macen kyauta don burge ta, wasu lokutan ma har da rawa yakan taka mata.
A cewarsu, yanayin kan iya zama mara dadi idan namijin ya kasa burge macen a lokacin saduwa, saboda tana iya kashe shi nan take ta kuma cinye shi.
Macen gizogizo na da baiwar saka kwai har 3,000 a lokaci daya.
Wasunsu kan mutu da zarar sun gama saka kwai, yayin da wasunsu har sai bayan kyankyashewa har su rika yawatawa lullube da sabbin kyankyasar.
Akwai darasi cikin rayuwar ‘Ankabuti’ (gizogizo) wanda hakan ya sa Alkur’ani Mai Girma ya buga misali da shi.
Domin sanin wannan darasi, mai karatu sai a dukufa bincike!
Sai wani makon idan Allah Ya kai mu.