Fara na daga cikin kwarin da ake iya gani a kowane lokaci kuma a ko’ina, a gida ko a daji.
Kwari ne masu tashi kasancewar suna da fiffike, kuma sun kai nau’uka sama da 11,000 da ake da su a fadin duniya, inji masana.
Tana da kafa guda shida da wasu ‘yan dogayen abubuwa guda biyu makale a kanta wadanta kan taimaka mata wajen tantance motsi.
Da yake kowace halitta na da baiwa da kuma sifoffin da ta kebanta da su, haka ma fara ma ba a bar ta a baya ba.
Masana kimiyyar da suka nazarci rayuwar wannan halitta, sun bayyana wasu sifoffin da suka gano a tattare da fara:
- Sun ce abin da watakila da yawa ba su sani ba game da fara shi ne, ido biyar gare ta, biyu daga ciki su ne wadanda ake iya gani a zahiri a kanta, su ne ke taimaka mata ganin wuri ta ko’ina. Sannan a tsakanin wadannan dogayen abubuwan nan guda biyu da take dauke da su a kanta, akwai kananan idanu guda uku wanda sai an lura da kyau za a iya gano hakan. Sai dai har yanzu masana sun kasa gano dalilin samun karin wadannan idanu ukun da fara ke da su balle gano aikin da suke yi.
- Fara na daga cikin kwarin da mutane kan ci. Hasali ma, wasu masana na ra’ayin ana samun wasu muhimman sinadarai a jikin fara masu amfani ga jikin dan Adam. Yankunan Asiya da Afirka da Amurka na daga cikin yankunan da ake cin fara sosai.
- A kasar Japan, fara babbar alama ce ta nasara. Sukan danganta fara mai launin kore da alamar samun tushen al’amari mai albarka da lafiya mai inganci da ci gaban matasa da sauransu.
- Sunan da aka bai wa fara a kimiyance shi ne ‘Caelifera’. Kuma kwari ne masu cin tsirrai da makamantansu.
- Ana da nau’ikan fara sama da 11,000 a fadin duniya.
- Halittu irin su tsuntsaye da beraye da kadangaru da sauransu kan zama babbar barazana ga rayuwar fara saboda farautarsu da sukan yi.
- Fara kan rayu tsawon shekara guda muddin ba ta fada a tarkon sauran manyan kwari ba.
- Sabanin sauran kwari wanda kunnuwansu ke makale a kai, lamarin ba haka yake ga fara ba. Kunnuwanta na makale ne a gefen cikinta. Su ke taimaka mata wajen jin sautin motsi.
- Kwari ne masu barna, musamman wajen cinye amfanin gona. Hakan kan auku ne idan ta hadu wuri daya ta yi yawa, sai ya zamana duk gonar da ta sauka, sai ta cinye amfanin ciki kaf.
- A wasu sassan duniya, akan yi amfani da fara a matsayin magani da dai sauransu.