Alhaji Dogara Isiyaka wani dattijo ne da ke zaune a garin Jos fadar Jihar Filato, ya bayyana wa wakilinmu cewa ya zo garin Jos ne sama da shekara 70. Tsohon ma’aikacin gandun daji ne da ya yi shekara 35 yana aiki kafin ya yi ritaya shekara 27 da suka gabata. Ya bayyana wa Aminiya cewa rayuwar da ta bambanta da ta yanzu:
Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?
Sunana Alhaji Dogara Isiyaka. Kuma an haife ni ne a garin Keffi, da ke Jihar Nasarawa fiye da shekara 120 da suka gabata. Daga cikin Sarakunan Keffi 15 na san 7. Sakunan Keffi da na sani, sun hada da Abubakar Burga wanda ya yi sarauta daga 1921-1923 da Abdullahi Maigari wanda ya yi sarauta daga 1923-1928 da Muhammadu Maiyaki wanda ya yi sarauta daga 1928-1933 da Abubakar Dan Amadu wanda ya yi sarauta daga 1933-1949 da Amadu Maikwato wanda ya yi sarauta daga 1949-1978 da Muhammadu Chindo Yamusa wanda ya yi sarauta daga shekara ta 1978-2015 da kuma wanda yake kai yanzu Shehu Chindo Yamusa. Kuma ni zuri’ar Sarkin Keffi Abubakar Burga ne.
A wajen mahaifinmu muna da yawa, amma yanzu abin da muka rage saura ni, da kannena mata guda biyu, daya tana da shekaru 81, dayar kuma tana da shekaru 72. Ina da ’ya’ya 14, maza 9 mata 5 da suke raye a duniya.
Ya ya maganar karatu?

Na yi karatun Alkurani da litattafan addinin Musuluci. Kuma na yi karatun boko na Elementari aji uku. A lokacin da na yi karatun addini, ina da kokari sosai domin babu karatun da za a koya mini, a sake tuna mini. Ina da shekara 32 na shiga yawan duniya. A Najeriya babu inda ban shiga ba. Kuma na yi kasuwanci iri daban-daban.
Lokacin da Turawa suka zo Keffi an ce Sarkin lokacin, Magaji Dan Yamusa ya kashe wani babban Soja Bature da aka turo, ko ka san lokacin da al’amarin ya faru?
Kwarai kuwa ina nan a garin, Sarkin Keffi Magaji Dan Yamusa ya kashe Kyaftin Moloney wanda shi ne Razdan da Turawa suka turo zuwa garin. Wannan al’amari ya faru ne a 1902, amma lokacin muna yara kanana ne.
Kamar yadda na samu labarin yadda al’amarin ya faru, an ce a wajen wani taro ne da aka yi tsakanin ayarin Razdan Kyaftin Moloney da ayarin Sarkin Keffi Magaji Dan Yamusa, takaddama ta tashi. Shi ne fada ya kaure, Sarkin Keffi Magaji Dan Yamusa ya sa takobi ya sare kan Kyaftin Moloney. Daga nan ya yi gudun hijira zuwa Kano, inda Sarkin Kano Alu na lokacin, ya ji dadi ya karbe shi hanu bibbiyu ya ba shi mafaka.
Kuma Turawan ba su yi komai ba, amma sun ci gaba da zuwa suna tafiya. Wadansu suna tafiya kan doki wadansu a kasa. Muna nan muna kallonsu, har suka yi karfi suka karbi mulki.
Bayan da Turawa suka mika mulki ga ’yan kasa, kana ina lokacin da aka yi juyin mulkin su Sardauna?
Ina nan a garin Jos aka yi juyin mulkin su Sardauna, domin yanzu ina da sama da shekara 70 zaune a nan garin. Na yi aikin gundun daji na tsawon shekara 50, kuma yanzu ina da shekara 27 da yin ritaya.
Zamanin wane Sarki ne ka zo Jos?
A lokacin da na zo Jos iyakar garin shi ne Dogon Agogo. Amma duk sauran kewayen garin daji ne. Kuma na zo garin ne zamanin Sarki Jos Isiyaku, na yi shekara 4 da wata 8 da zuwa ya rasu. Kuma Sarkin Jos Isiyaku ne ya nada Gbong Gwom Jos Ram Pam a matsayin Sarkin kabilar Birom na farko a lokacin. Bai kai shekara 3 da nadawa ba, Sarkin Jos Isiyaku ya rasu.
Yaya aka yi ka kama aiki a Hukumar Gandun Daji?
Bayan da na zo nan Jos ne na kama aiki da Hukumar Gandun Daji. A da duk gandun dajin Najeriya na karkashin wannan hukuma ce. Na yi lebura na tsawon shekara 10. Daga nan aka dauke ni cikakken ma’aikaci, na yi shekara 35. A ranar da na yi ritaya, a ranar ne aka sake daukata a matsayin kwangila.
Na kai har aka ba ni matsayin shugaban hukumar. A lokacin mu ne muka auna Najeriya baki daya, muka fitar da hanyoyin shanu, ta yadda babu saniyar da za ta shiga gonar wani manomi. Daga karshe na ce na gaji da aikin, su kuma suka ce ba za su bar ni ba. Sai da na yi shekara 2 ba na karbar albashi don su kyale ni amma ba su kyale ni ba. Daga karshe dai na kwashe kayana daga wajen, sannan suka kyale ni.
Yaya za ka kwatanta yadda gwamnati ta dauki gandun daji da itatuwa a da da yanzu?

Ai yanzu a cikin kashi dari na aikin Gandun Daji ba a iya yin kashi 10. A da ko itace daya ka sare, idan jami’in gandun daji ya kama ka, zai tuhume ka. A da ba ka isa ka je daji ka sari itace ba. Idan aka kama mutum za a iya daure shi. A da duk wani gari da ka sani a Najeriya yana da gandun daji. Daga baya ne, duk aka bi aka sassare
Yaya za ka bayyana muhimmanci itatuwa a kasar nan?
Itatuwa suna da amfani mai yawa. Idan gidan mutum babu itace, iska za ta iya kwashe gidan baki daya. Kuma itace yakan ba mu iskar da muke shaka mai kyau, wadda za ta gyara mana lafiyarmu.
Wadanne manyan mutane ne ka yi zama da su a wannan gari?
Na zauna da mutane da dama a wannan garin. A bangaren malaman addinin Musulunci, mun zauna da marigayi Sheikh Isma’ila Idris. Yadda muka hadu da shi shi ne lokacin da ya zo yana wa’azi yana bata darika, a lokacin ina Darikar Tijaniya, kuma dukan rumfunan tafsiri da ake yi na darika a Jos, ni nake yin su, sai ban ji dadi ba. Akwai wani malami ana kiransa Nabakura, sai suka yi mukabala da marigayi Sheikh Isma’ila Idris kan darika, sai ya kure malamin. Daga lokacin na fita daga darika.Tun daga nan muka ci gaba da hulda da marigayi Sheikh Isma’ila Idris, kowa ya sani a garin nan. Yana zuwa har gidana wani lokacin yakan kai har karfe 12 na dare, har Allah Ya karbi rayuwarsa.
Bayan haka akwai Sheikh Sani Yahya Jingir, shi na fara sanin mahaifinsa ne Malam Yahya Jingir. Nakan tashi daga nan Jos in tafi har wurinsa a garin Jingir. Samun mutum irin Malam Yahya Jingir yana da wuya, domin mutum ne wanda za ka je wajensa, ko bai sanka ba, zai zaunar da kai ku yi hira. Idan za ka tashi idan yana da Naira 100, zai iya dauka baki daya ya ba ka.
Duk lokacin da Sheikh Sani Yahya ya zo, yakan zo ya same ni, tare da mahaifinsa. Babu shakka muna da dangantaka mai karfi tsakanina da Sheikh Sani Yahya Jingir, domin yanzu akwai wata riga da ya dinka mini, wadda duk garin nan zai yi wuya ka samu mai aikinta. Bayan haka a bangaren manyan ma’aikata da ’yan siyasa. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a zamanin gwamnatin Ibrahim Babangida Wazirin Jama’a Alhaji Aliyu Muhammed ya zo nan garin Jos ya zauna a gidana ya yi karatu har ya gama, saboda mun yi hulda da mahaifinsa. Bayan haka muna hulda da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu da babban dan kasuwar nan marigayi Alhaji Shehu Tabaco har Allah Ya yi masa rasuwa.
A takaice na zauna da mutane da dama a wannan garin tun daga kan ma’aikatan gwamnati da malaman addini da ’yan kasuwa da sauransu.
A matsayinka na wanda ya ga jiya ya ga yau, yaya za ka kwatanta mutane da na yanzu?
Gaskiya akwai bambanci domin a da idan mutane suka ce maka Allah daya ne, sai ka yarda. Amma yanzu idan mutane suka yi maka rantsuwa da Allah da wuya ka yarda. Domin yanzu cikin mutum 100 da suka karanci addini, idan suka yi maka magana suka rantse da Allah, zai yi wuya ka samu mutum 10 da suke da gaskiya. Mutanen yanzu ba su da gaskiya. Yanzu mutum ne zai rantse maka da Allah da Alkur’ani kan karya. Yanzu idan kuka yi wata hulda da mutum, zai yi maka magana ka yarda amma karya yake yi. Yanzu babu gaskiya da rikon amana a kan magana ko dukiya.
Amma mutanen da ba haka suke ba. A da idan ka yar da kudi, wani ya tsinta haka zai rike kudin yana neman mai kudin. Haka kuma idan mutum ya yar da kudi, sai kudin su yi kwana uku a wajen da aka yar, babu wanda ya dauka. Amma yanzu mutane kowa ya mayar da hankalinsa kan neman dukiya. Shi ya sa yanzu zalunci ya yi yawa.
Haka kuma ba za ka hada masu arzikin da, da na yanzu ba. Masu arzikin da suna fitar da zakka, amma na yanzu ba sa yi. Yanzu za ka ga mutumin da ya kamata ya fitar da zakkar Naira miliyan daya, sai ya fitar da dubu 100 kawai.
Har ila yau ba za ka iya kwatata zaman lafiya da, da yanzu ba. A da sai ka kwanta kan hanya ka yi barcinka, babu abin da zai same ka, ko da kudi a jikinka. Yanzu haka ba zai yiwu ba, kwanciyar hankali ya wuce, babu wanda zai ce maka yana zaune lafiya.Amma a da da masu kudi da talakawa kowa yana jin dadi, hankali kwance.
Ko akwai sauran mutanen da ka samu a nan Jos a yanzu?
Duk mutanen da na samu a garin Jos lokacin da na zo, babu wanda yake raye a yanzu, sai dai ’ya’yansu da jikokinsu. Daga Dogon Agogo zuwa abin da ya shiga cikin garin Jos, zuwa babbar Kasuwar Jos duk wadanda na same su sun rasu.
Wace kira kake da shi ga jama’a?
Nasiha ta ga dukan al’umma ita ce mu yi hakuri, mu roki Allah dukan abin da muke so, domin Shi ne Mai bayarwa. Babu wanda zai iya yi maka arziki sai Allah. Don haka mu rike Allah, kuma mu rike gaskiya.