✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwa cikin Ruhu

Barkanmu da sake saduwa cikin makon Ista wato makon tunawa da mutuwa da tashin Yesu Almasihu don ceton dukan duniya. To, wani irin rayuwa ne…

Barkanmu da sake saduwa cikin makon Ista wato makon tunawa da mutuwa da tashin Yesu Almasihu don ceton dukan duniya. To, wani irin rayuwa ne ya kamata mu yi bayan wannan fansa da Yesu ya yi mana bisa gicciye?  A takaice amsar ita ce zaman tsarki wato bin tafarkin Ubangiji ko kuma mu ce rayuwa cikin Ruhu ta wurin bin gurbin da Yesu Almasihu ya bar mana.
Bin gurbin Yesu Almasihu abu ne da ya kamata ya zama mana rayuwa ta yau da kulum a zamanin da muke ciki a yau, domin shi ne hanyar nasara, ceto da kuma rai mara matuka.
Gama Yesu ya ce shi ne hanya, shi ne gaskiya kuma shi ne rai, ba mai zuwa wurin uban sai ta wurinsa. (Yahaya 14:6). Shi ya sa Yesu ya bar mana gurbi mu bi; wato tafiya cikin ruhu-rayuwar tsarki, ba rayuwar mutuntaka ko son jiki ba, kamar yadda manzo Bulus ya fadi a littafin Galatiyawa 5:16-25  “Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba, don halin mutuntaka gaba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gaba da halin mutuntaka. Wadannan biyu gaba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so. In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, Shari’a ba ta da iko da ku, ke nan. Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci da aikin lalata da fajirci da bautar gumaka da sihiri da gaba da jayayya da kishi da fushi da son kai da tsaguwa da hamayya da hassada da buguwa da shashanci da sauransu. Ina fadakar da ku kamar yadda na fadakar da ku a da, cewa masu yin irin wadannan abubuwa, ba za su samu gado a Mulkin Allah ba.”
A nan mun ga abubuwan da suka kamata mu gujewa idan har muna son mu ci nasara a rayuwarmu na bin gurbin Yesu don mu samu rai na har abada. Abubuwan da aka lisafta mana na halin mutuntaka abubuwa ne na kyama ga mu mutane ma, amma sai ka ga don son kai da kwadayi mukan yi sakaci har Shaidan ya samu zarafin mamaye rayuwarmu har mu bar bin tafarkin Ubangiji.
Bari kuma muga abubuwan da zaman Ruhu ke dauke da su idan muka ci gaba a aya ta 22 – 25 cikin litafin Galatiyawa 5 “Albarkar Ruhu kuwa ita ce kauna da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da kuma kamun kai. Masu yin irin wadannan abubuwa, ba dama shari’a ta kama su. Wadanda kuwa suke suna Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha’awoyi iri-iri. In dai rayuwar tamu ta Ruhu ce, to, sai mu tafiyar da al’amuranmu ta wurin ikon Ruhu. Kai, abubuwan ban sha’awa ne kwarai da gaske ga mu mutane ma. Misali a zamaninmu na yanzu idan har muna da kauna da hakuri da kirki da nagarta da makamantansu, babu shakka irin abubuwan da ke faruwa a fadin duniyar nan tamu ba za mu gansu ba, komai a bayyane yake, kowa ya san da wannan, amma da yake sha’awar kayan duniya da na jiki sun shiga zuciyar mutane da yawa, sai kowa ya bi nasa tafarkin ya manta da hanyar da Yesu Almasihu ya nuna mana wato zaman Ruhu ko tsarki.
Sai mu lura mu guje wa irin abubuwan da Littafi Mai tsarki ya fadi su ne halin mutuntaka a inda muka karanta,  mu bi na Ruhaniya don mu samu rai na har abada.
A karshe za mu ga abin da litafin Afisawa 2:1-6; ke fadi “Ku kuma ya raya ku sa’’ad da kuke matattu ta wurin laifuffuka da zunubanku, wadanda da kuke a ciki, kuna biye wa al’amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu. Dukkan mu damun zauna a cikinsu, muna biye wa sha’awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga dabi’a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran ’yan Adam. Amma Allah da yake Mai yalwar jinkai ne, saboda matsananciyar kaunar da Yake yi mana, ko a sa’ad da muke matattu ma ta wurin laifuffkanmu, sai Ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku), a cikin Almasihu Yesu kuma ya tashe mu tare, har ya ba mu wurin zama tare a samaniya.
Sai mu yi nazari a kan wadannan abubuwa, muna tuna da mutuwar Yesu Almasihu da kuma tashinsa don mu samu rai madauwami.

Ubangiji Allah Ya albarkace mu, amin.