Rayo Vallecano ta lallasa manyan kungiyoyin kwallon kafar Sifaniya wato Real Madrid da Barcelona a kakar tamaula ta La Liga ta bana.
Ranar Laraba Rayo ta doke Barcelona 2-1 a wasan mako na 31 a gasar La Liga da suka fafata.
- Buhari ya je wurin fareti sanye da kakin soja
- An kori hafsoshin ’yan sanda 3 daga aiki, an rage wa 5 matsayi
Rayo ce ta fara cin kwallaye ta hannun Alvaro Garcia da Francisco Garcia daga baya Barca ta zare daya ta hannun Robert Lewandowski.
A wasan farko a bana da suka buga da fara La Liga tsakanin Barca da Rayo sun tashi 0-0 ranar 13 ga watan Agusta a Camp Nou.
Ko a kakar bara ta 2021/22 Rayo ce ta doke Barcelona gida da waje kowanne da cin 1-0.
Bayan da Barca ta ci Rayo wasa 13 a jere har da karawa biyar da take cin kwallo biyar ko fiye da hakan a baya, yanzu batun ya sauya da kyar take kwatar kai.
Domin Barcelona ta kasa cin Rayo a karawa hudu kenan baya da suka yi har da kasa zura kwallo a raga a uku daga ciki.
Wasan da Rayo ta ci Barcelona 1-0 a karawar farko a La Liga a bara a cikin Oktoban 2021 ranar Laraba ta yi nasarar.
Ranar 7 ga watan Nuwambar 2022 Rayo ta doke Real Madrid 3-2 a wasan farko da suka kara a bana a babbar gasar tamaula ta Sifaniya a tsakaninsu.
Rayo ta ci kwallayen ta hannun Santiago Comesana da Alvaro Garcia da Oscar Trejo a bugun fenariti.
Ita kuwa Real Madrid ta zare biyu ne ta hannun Luka Modric a bugun daga kai sai mai tsaron raga da wadda Eder Militao ya ci.
Ranar 24 ga watan Mayu Real Madrid za ta karbi bakuncin Rayo a karawa ta biyu a bana a La Liga a Santiago Bernabeu.
Rayo Vallecano ta hada maki 43 tana mataki na tara bayan karawa 31 a La Liga.
Barcelona ce ta daya a kan teburi mai maki 76, sai Real Madrid ta biyu da maki 65.