✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasuwar Sanatan mazabar Daura ta sake jijjiga al’umma

A shekaraniya Laraba da ce Allah Ya yi wa dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Mazabar Daura, Injiniya Mustafa Bukar Madawakin Daura rasuwa. Sanatan ya rasu…

A shekaraniya Laraba da ce Allah Ya yi wa dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Mazabar Daura, Injiniya Mustafa Bukar Madawakin Daura rasuwa. Sanatan ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a Asibitin Turkiyya da ke Abuja. Marigayin yana daya daga cikin jinin sarautar Daura, inda ya taba neman sarautar bayan rasuuwar Sarkin Daura, Alhaji Muhammadu Bashar. 

Sanata Bukar  ya zama Sanata ne bayan ya lashe zaben shekarar 2015 a karkashin Jam’iyyar APC. Musatafa Bukar kafin rasuwarsa ya taba zama Kwamishinan Ruwa a Jihar Katsina, kuma ya yi Darakta a Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya inda daga can ya ajiye aiki ya shiga harkokin siyasa. An haifi Injiniya Bukar Mustafa a watan Disamban 1954 a garin Daura, ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 12. kuma an yi jana’izarsa a garin Daura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Rasuwar Sanatan ta bar  babban gibi a masarautar Daura da Jihar Katsina da Najeriya kamar yadda wadansu na kusa da marigayin suka bayyana. Sun ce mutum ne mai taimakon jama’a a koyaushe.