✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasuwar Sanata Mustafa Bukar ta bar gibi babba – Sarkin Kudu

Daya daga cikin ’yan uwan Marigayi Mustafa Bukar, Sanata mai wakiltar Katsina ta Arewa, Alhaji Abdullahi Bukar ya bayyana rashin nasa a matsayin babban gibi…

Daya daga cikin ’yan uwan Marigayi Mustafa Bukar, Sanata mai wakiltar Katsina ta Arewa, Alhaji Abdullahi Bukar ya bayyana rashin nasa a matsayin babban gibi mai wuyar cikewa. Alhaji Abdullahi Bukar wanda har ila yau shi ne sarkin Kudun Daura, ya ce ayyukan alheri da marigayin ya aiwatar ga al’ummarsa a yankunan kananan hukumomi 12 da ya wakilta da ya kunshi masarautar Daura da ta Katsina da ya hada har da samar da gurabun aiki ga matasa, ya ce ba su kirguwa. dan uwan marigayin ya ce Sanata Mustafa Bukar ya kuma yi sanadiyyar sada yankin da ayyuka irin na tituna da samar da ruwan sha, inda ya yi fatan hakan ya zame masa sanadin shiga aljannah.

daya daga cikin ’ya’yan marigayin mai suna Ibrahim Mustafa Bukar ya ce babban abin da zai tuna mahaifin nasu da shi shi ne yawan nasihar da ya ke yi masu na su riki addini a dukkan al’amura, sannan su kasance masu sada zumunci. 

Sanata Mustafa Bukar wanda ya rasu a ranar 4 ga watan nan, ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 12 kamar yadda wani dan uwan marigayin, Alhaji Nuhu Bukar ya tabbatar. Daga cikin wadanda suka kai gaisuwa da karban ta’aziyya a mahaifarsa ta Daura, har da shugaban kasa Muhammmadu Buhari wanda marigayin ke matsayin amininsa kuma mai wakiltar yankin da ya fito.