Kusan watanni uku ke nan da samun sabani tsakanin Gwamnatin Jihar Zamfara, da hukumar samar da wutar lantarki, ta kasa, saboda dimbin bashin da hukumar ke bin gwamnati.
Wannan lamari ya zama silar katse wutar duk wata ma’aikatar Jihar Zamfara, wadanda suka hada da ma’aikatu da makarantannin gwamnati da asibitoci mallakar Jihar Zamfara da sauransu.
Hakan ya sa yanzu daukacin wadannan wurare suke wuluk….!
Babbar damuwar ita ce, asibitocinmu na Jihar Zamfara, inda majinyatan ke matukar bukatar wutar domin samun wadatacciyar iskar fanka, musamman a wannan lokacin da muke fama da matukar zafi.
Hakazalika ma’aikatan asibitin na matukar bukatar wutar, wanda sakamakon rashin wutar lantarki da ake fama da shi a yanzu ana iya rasa rayuka da dama kasancewar ba kowane marar lafiya ne ke iya sayen iskar karin numfashi ba, (OdYGEN).
Kuma duk marar lafiyar da wannan lalurar ta bukatar shan iskar karin numfashi (Odygen) ta same shi a yanzu akalla zai iya amfani da ganga 8 a rana, ko fiye da haka. Sannan duk karamar ganga kudinta #2000 ne. Amma da za a samu wutar lantarki za a iya yi wa wadannan marasa lafiyar amfani da wata na’urar ba da iska kyauta, wanda ake kira “Odygen Concentrator.”
Ko a ranar Litinin 31-7-2017 na ziyarci asibitin mata da kananan yara na Sarki Fahad Ibn Abdul’azizu da ke Samuru Gusau, domin yin wani awon jini, Kai Tsaye aka shaida mini cewa; “ wannan awon sai da wuta ake yinsa. Kuma ba mu da ita.” Dolenmu sai mun tafi a asibiti mai zaman kanta. Wannan ke nan!
Abin fargabar da tashin hankali, ba wasu wadatattun kudin gudanarwa ne Gwamnatin Jihar Zamfara ke warewa ma’aikatu ba. Asibitocin Jihar Zamfara na daga cikin ma’aikatun da ke fama da wannan matsalar. Domin a irin asibitin kwararru na YARIMAN BAKURA, wanda shi ne mafi girma da wadatuwar kayan aiki da kuma ake nema wa gwamnatin jihar kudi. Amma ko a irin wannan asibitin ba a iya tayar da injin samar da wutar na sa’o/’i shida, a kullum.
Uwa-uba kananan asibitinmu da wasunsu ko injin ba su da shi balantana su tayar da shi.
Sakamakon haka likitoci da malaman jinya (Nurses) suna gani mutane su dinga mutuwa babu.