✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin tsaro: Za mu hada kai da gwamnonin jam’iyyun adawa — Gwamnonin APC

Gwamnonin jam’iyyar APC sun yanke shawarar zama tsintsiya madaurinki daya wajen yin aiki tare da takwarorinsu na jam’iyyar adawa ta PDP da APGA don magance…

Gwamnonin jam’iyyar APC sun yanke shawarar zama tsintsiya madaurinki daya wajen yin aiki tare da takwarorinsu na jam’iyyar adawa ta PDP da APGA don magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar.

Gwamnan Jihar Kebbi kuma Shugaban Kungiyar PGF ta Gwamnonin jam’iyyar APC, Atiku Bagudu, cikin wata makala da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata mai taken “Ceto Daliban GSSS Kankara da aka sace” y ace ceton ya tabbatar da iyawa da cancantar hukumomin tsaron Najeriya wajen tabbatar da bai wa kasar nan kariya.

A makonni biyu da suka gabata ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da daruruwan dalibai na Makarantar Sakandiren Kimiyya da ke garin Kankara a jihar Katsina, inda bayan kwanaki kadan jami’an tsaro da Gwamnonin Jihohin Katsina da Zamfara suka yi ruwa da tsaki wajen ganin daliban sun kubuta cikin ruwan sanyi ba tare da rai ko guda ya salwanta ba.

Da wannan ne Gwamnonin jam’iyyar APC suka ce, “za mu tabbatar da cewa a matsayinmu na shugabanni, mun yi aiki tare da dukkanin gwamnoni, shugabannin siyasa, da wadanda ba na siyasa ba domin maido da zaman lafiya a dukkan sassan kasar, ba tare da la’akari da wani bambanci ba.”

“Kasar Najeriya ta dukkan al’ummar da ke cikinta ne kuma dole ne a tabbatar da ita a matsayin kasa daya tilo wacce ba za ta wargaje ba karkashin ikon Allah kamar yadda kundin tsarin mulkinta na 1999 ya tabbatar,” inji gwamnonin.

“A yanzu bayan ceto daliban, muna yi wa Allah Madaukakin Sarki da duk wadanda suka bayar da gudunmuwar nasarar kubutar da wannan dalibai daga hannun ’yan bindigar, musamman, gwamnatin Jihar Katsina, karkashin jagorancin Mai Girma, Aminu Bello Masari.”

“Duba da irin muhimmiyar rawar da hukumomin tsaronmu da sauran shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu suka taka wajen ceto daliban, hakan ya nuna cewa kokarin da ake yi na magance matsalar tsaro a kasarmu wani nauyi ne da ya ke bukatar hadin kai, azama da daukar mataki na gaggawa.”