An kai wa masu zanga-zangar neman kawo karshen matsalar tsaro a Arewacin Najeriya da ke gudana a Kano hari, tare da jikkata akalla mutum 30.
A safiyar Alhamis ne daruruwan mutane tare da rakiyar ’yan sanda suka fita kan tinunan Kano inda suke gangamin neman karshen matsalar da ta addabi yankin.
- #EndSARS: Sojoji sun yi wa masu tayar da rikici kashedi
- Matasa sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan SARS a Kano
“Ba mu fi mita 500 daga inda muka fara tattakin lumanar ba sai ’yan daba suka fara bin mu a guje, suka ji wa mutum kusan 40 rauni, suka yayyaga kwalayenmu”, inji daya daga cikin masu zanga-zangar ta #Endinsecuritynow, Dokta Muhammad Bello Nawaila.
‘Yan sanda sun yi batar dabo
Ya ce “Abin mamakin shi ne yadda ’yan sandan da ke mana rakiya suka yi layar zana a lokacin da muka matukar bukata.
“Su ne ya kamata su yi mana jagora suna kuma kula da hanya domin mun sanar da su ta hanyar da za mu bi.
“Da ’yan dabar suka kawo mana hari sai muka nemi ’yan sanda muka rasa, sai bayan da aka ji wa mutum 30 zuwa 40 rauni kafin suka sake dawowa”, inji Dokta Nawaila.
Makamanciyar zanga-zangar lumanar ta #Endinsecuriynow na gudana a jihohi 19 na Arewacin Najeriya, yankin dsa matsalar tsaro ta yi kamari.
Arewa maso Gabas ya shekara 11 yana fama da matsalar ta’addancin kungiyar Boko Haram wanda wani bangare nata ya yi mubaya’a ga kungiyar ISWAP.
Ayyukan ’yan bindiga da barayin shanu da masu garkuwa da mutane kuma sun addabi Arewa ta Yamma.
Baya ga haka, rikicin kabilanci da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da rikicin manoma da makiyaya sun fi kamari a Arewa ta tsakiya.