Fadar Shugaban kasa ta bayyana Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF, Farfesa Ango Abdullahi a matsayin jagoran tafiya mara katabus.
Mai ba wa Shugaban Kasa Shawara kan Yada Labarai, Femi Adesina ya yi martanin biyo bayan takardar da NEF ta fitar tana zargin gazawar gwamnati wajen bagance matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya.
Ango Abudullahi a cikin takardar ya ce ci gaban matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ya nuna Shugaba Buhari da gwamnonin jihohin sun gaza wajen sauke nauyin dake kansu na kare jama’a.
A takardar martanin, Femi Adesina ya ce Shugaba Buhari ya dukufa wajen samar wa Najeriya abin da ya dace, kuma ‘yan Najeriya sun san gaskiyar halin da ake ciki.
- ‘Rashin kwarewa da mugayen fadawa su ne matsalar Buhari’
- Harbe-harbe a Aso Rock: Doka za ta yi aikinta —Buhari
Martanin nasa ya ci gaba da cewa har yanzu suna daukar NEF a matsayin taron mutum daya kuma “mara nagartattun mambobi sannan shugabanta fanko ne”.
Ya ce Kungiyar NEF da Ango Abdullahi ke ikirari ta dade da nuna adawarta ga Shugaba Buhari a fili tun kafin zaben 2019 amma duk da haka ya kayar da su a zabe.
Don haka ya ce maganganun kungiyar ta NEF ba su da wani tasiri.