Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce hare-hare da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan jihar wasu ne ke ɗaukar nauyinsu ba rikicin manoma da makiyaya ba ne.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen taron baje-kolin kayayyakin ado da fasaha da Tincity Fashion ta shirya mai taken, “The Plateau Experience”, da aka yi a ranar Juma’a a Abuja.
- An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe
- Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya bayar da rahoton cewa, a ranar 2 ga watan Afrilu, wasu ’yan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Manguno, Daffo da Josho na ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar.
Maharan sun kashe mutane da dama tare da lalata gidaje da wasu kadarori na miliyoyi.
Mutfwang, wanda ya jaddada cewa hare-haren an tsara shi ne, ya yi alƙawarin cewa gwamnati da hukumomin tsaro sun tanadi matakan daƙile afkuwar lamarin nan gaba.
“Ina so in gode muku da kuke nan domin goyon bayanku da kuma karrama Filato tare da halartarku a wannan taron, ba mu ɗauki wannan haɗin kai da wasa ba.
“Mun yi tunanin dakatar da wannan taron ne saboda yanayin tsaro da jihar ke fama da shi, amma mun yanke shawarar kada lamarin ya lalata mana kyawawan abubuwan da ya kamata mu yi na taron biki.
“Kuma dole ne in ce manufar maƙiya ita ce jefa jihar cikin ruɗu da baƙin ciki, amma za mu kauda manufarsu ba za mu ba damar yin abin da suke so ba.