✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rashin tawakkali’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan alheri kuma kuna lafiya. A yau na kawo muku wani labari ne mai taken:  ‘Rashin tawakkali.’  Labarin…

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan alheri kuma kuna lafiya. A yau na kawo muku wani labari ne mai taken:  ‘Rashin tawakkali.’  Labarin na kunshe ne da yadda ya kamata Manyan Gobe su zama masu godiya da tawakkali ga iyaye don samun albarka.
Taku: Amina Abdullahi
 
An  yi wani dan kasuwa mai suna Ali. Yana da mace da ’ya’ya biyu. Suna da rufin asiri daidai gwargwado. Sannan Allah Ya ba su wata  kaza wadda take yin kwai kullum. Wani abin mamaki da burgewa da daukar hankali shi ne kazar tana yin kwai ne na gwal.
Saboda hadama Ali bai gamsuwa da kwai daya na gwal da take saka masa kullum ba. Sai ya yanke shawarar ya yanka kazar don ya kwashe dukan kwan gwala-gwalan da ke cikinta.
Washegari, kazar ta yi kwai kamar yadda ta saba. Don rashin godiya da hadama da gaggawa, sai ya samu wuka mai kaifi, ya yanka, ya farke cikinta ko zai kwaso kwayayen.  Nan idonsa ya raina fata, inda ya ga ba komai a cikin sai kayan ciki da jini yana zuba.
Kafin wani lokaci ya rasa kwan da yake samu a kullum.  
Hadama ta sanya Ali ya rasa alherin da yake samu daga kazar.
Da fatan Manyan Gobe sun dauki darasi daga wannan labari.