Jam’iyyar adawa ta ADC, ta ce tana cikin damuwa kan yadda harkar ilimi ta taɓarɓare a Jihar Yobe.
Shugaban jam’iyyar a jihar, Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa ne, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Damaturu.
Ya ce tsarin ilimi a Jihar Yobe ya lalace ƙwarai, inda ya ce lamari shi ne ya fi muni sama da yadda aka taɓa gani a shekarun 1950.
A cewarsa, makarantun gwamnati da dama ba su da isassun malamai, kayan koyo da koyarwa, sannan kuma ajuwuwa sun lalace.
A cewarsa a wasu makarantu, ɗalibai sun yi yawa sama da yadda za a iya kula da su.
Farfesan, ya ƙara da cewa dubban mutanen jihar sun rasa matsugunansu, yayin da ’yan gudun hijira ke fama da rayuwa mai tsanani.
Ya ce wasu daga cikinsu har sun zama mabarata, inda ya zargi hakan da gazawar shugabanci.
Ya buƙaci jama’ar Jihar Yobe da sauran ’yan Najeriya su goyi bayan tafiyar jam’iyyar ADC domin gyara shugabanci da yi wa al’umma aiki.
“Muna buƙatar sabuwar hanyar dogaro da gaskiya, cancanta da riƙon amana,” inji shi.
“Muna kiran dukkanin ’yan Yobe da ’yan Najeriya da su mara mana baya domin dawo da martabar shugabanci da makoma mai kyau.”