✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rashin shigowar damina da wuri ne ya jawo tsadar Dankalin Turawa’

Wani mai sayar da Dankalin Turawa a kasuwar ‘yan Dankali da ke garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato, Malam Yahaya Abdullahi dan Garko, ya bayyana…

Wani mai sayar da Dankalin Turawa a kasuwar ‘yan Dankali da ke garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato, Malam Yahaya Abdullahi dan Garko, ya bayyana cewa rashin samun ruwan sama a kan kari ne ya jawo tsadar da Dankalin Turawan a bana.

dan kasuwan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya kwanakin baya, inda ya ce: “Na yi kamar shekara 30 ina sayar da Dankali a wannan kasuwa, amma ban taba ganin irin tsadar da Dankali ya yi ba, irin wanda ya yi a bana.”
“Domin a bana ne muka sayo buhun ledar Dankali kan kudi har naira dubu 17 daga karamar hukumar Bokkos muka zo muka rika sayarwa kan naira dubu 19. Wannan ya faru ne saboda rashin shigowar damina da wuri,’’ inji shi.
Kodayake, ya ce, “a yanzu damina ta fadi farashin Dankalin ya fadi ya dawo buhun leda naira dubu 10. Ya ce babu shakka da ruwan sama yazo da wuri da dankali bai yi wannan tsadar ba. A gaskiya a bana ‘yan kasuwar da suke sayar da dankali sun sha wahala, amma su manoman da suke nomawa sun sami kudi’’.
A zantawarsa da wakilinmu, shugaban ‘yan kasuwar Dankali da ke Kasuwar ‘Yan Doya a garin Jos, Alhaji Zakari Abdullahi ya bayyana cewa rashin saukar ruwan sama da wuri ne ya kawo matsalar karancin Dankali turawa a fadin kasar nan.
Ya ce: “A duk shekara kafin a shiga watan azumi sabon dankali yakan shigo kasuwa, amma a bana saboda rashin zuwan ruwan sama da wuri, ya sa bai zo ba, don haka farashin buhun ledar taki ya haura zuwa har naira dubu 17 a a kauyuka. Mu kuma mun sayar dashi naira dubu 19 zuwa dubu 20,” inji shi.