✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin lafiyar Shugaba Buhari ce dalilin shigata Musulunci -Rabaran Fada Simon

Ko za ka fara bayyana mana kanka? Sunana a yanzu Abubakar, sunan da na zaɓa ke nan bayan na Musulunta, domin a baya sunana Rabran…

Ko za ka fara bayyana mana kanka?

Sunana a yanzu Abubakar, sunan da na zaɓa ke nan bayan na Musulunta, domin a baya sunana Rabran Simon Paul. Ni ɗan asalin Jihar Imo ne kuma ina zaune ne a garin Shagamu, kuma ni Rabaran Fada ne a Cocin Angilika kafin in karɓi Musulunci.

Ko me ya sa ka shiga Musulunci?

Wannan abu daga Allah ne, ba yin mutum ba ne, nufi ne na Allah, domin akwai wani lokaci a baya wato lokacin da aka fitar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ƙasar waje domin nema masa lafiya. To, a wannan lokacin ƙungiyarmu ta Kirista ta kira mu, inda aka tara mu limamai, aka umurce mu da yin azumi da wasu addu’o’i, da zummar cewa Shugaba Buhari ba zai dawo Najeriya da ransa ba. Suka ce muddin muka yi wannan abin, babu yadda za a yi Shugaba Buhari ya dawo kasar nan da ransa. To, ni a lokacin sai na faɗa masu cewa zan yi abin da suka umurce mu, amma idan har aka samu akasi Buhari ya dawo ƙasar nan da ransa, to ni zan musulunta.

Haka kuwa aka yi, domin tun muna jin jita-jitar dawowar Shugaban kasa, wata rana ina zaune a gidana ina kallon talabijin, kwasam sai ga labarin dawowarsa. Ina ganinsa da idanuna sai da na saki fisari a wando, daga inda nake a zaune. Nan na ruɗe, na kiɗime, ina rayawa a zuciyata cewa yanzu ni ma zan koma cikin masu sanya goshinsu a ƙasa ke nan?

To, haka aka yi, ina cikin wannan hali sai wata rana na kwanta barci. Nan cikin barci sai na ga wanni mutum ɗauke da babban carbi ya nufo ni yana cewa ina alƙawarin da ka ɗaukar wa Allah? Kada fa ka manta da alƙawarin da ka yi. Bayan da gari ya waye sai na samu Sarkin Hausawan Shagamu, na ce masa na zo in shiga Musulunci, inda ya kai ni wajan Limamin Masallacin Juma’a na garin Sabo-Shagamu, wanda a wajansa na karɓi Musulunci, bayan ya yi mani bayanin sharuɗansa; ya kuma ba ni wasu littattafan koyan addinin.

To, a wane hali kake ciki a yanzu?

To, alhamdu lillahi, ina cikin Musulunci tare da ’yan uwa Musulmi a nan inda na sami mafaka na ɗan wani lokaci a garin Asaba kuma tun kafin in shiga Musuluncin ina sane da cewa da zarar na shiga zan haɗu da ƙalubale da dama daga ’yan uwana da ƙungiyarmu. To, ni ban damu da halin ƙuncin da zan shiga ba, domin koda zan rasa raina ne a kan addinin Musulumci to na rabauta. A lokacin da na karɓi Musuluncin, da na koma wajan ’yan uwana a can garin Shagamu, sun gan ni da Alƙur’ani da carbi a hannu sai suka gane ashe abin da na faɗa da gaske nake, sai suka kulle ni a wani ɗaki suka ɗaure ni ba abinci ba ruwa har na tsawon wasu lokuta. Daga bisani suka mayar da ni garinmu a Jihar Imo, inda daga nan na gudo zuwa Shagamu. Na yi tunanin za su sake zuwa su kama ni, sai na sami mafaka a garin Asaba, yanzu a nan nake zaune na ɗan lokaci.

To, mene ne burinka a yanzu?

Burina shi ne samun ilimin addinin Musulunci, fatan da nake da shi ke nan. Ina son in samu waɗanda za su koya mani addinin yadda ya kamata, har ni ma in ba da tawa gudunmawar wajan yin kira zuwa ga addinin, domin ina da sani a addinin Kiristanci, idan na samu ilimin addinin Musulunci, zan ba da gudunmawa wajan kira ga addinin.