Akwai yuwuwar a fuskanci karancin man fetur a Najeriya sakamakon umarnin da Kungiyar Direbobi Masu Dakon Mai ta Kasa (PTD) ta ba mambobinta su fara yajin aiki saboda rashin kyau da kuma lafiyar manyan hanyoyi a Najeriya.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar ta fitar ranar Litinin, dauke da sa hannun Shugabanta, Kwamared Salmon Akanni Oladiti da kuma Sakatarenta, Sunday Ochibe Jivwie.
- Kwararowar makamai: Sojoji na so a gina ganuwa a kan iyakokin Najeriya
- Zauna-gari-banza sun kona motar tumatir a Enugu
Kungiyar dai ta ce bayan tattaubna muhimman batutuwa, ta amince mambobinta su sake dawo da yajin aikin da suka dakatar a watan Mayun 2021.
“A sakamakon haka, dukkan direbobin dakon mai su fara yajin aiki daga ranar 27 ga watan Satumban 2021, a shirye-shiryen dakatar da dukkan ayyukan kungiyar daga ranar takwas ga watan Oktoban 2021, matukar Gwamnatin Tarayya ta gaza magance bukatunmu guda uku,” inji sanarwar.
Kungiyar direbobin ta ce mambobinta sune na farko da illar rashin kyan hanyoyi ya fi shafa a duk fadin kasa, lamarin da yake kai su ga asarar rayuka da ta dukiyoyi.
Idan dai yajin aikin ya tabbata, akwai yuwuwar a sami karancin man fetur sakamakon rashin dakon man daga rumbunan adana su, mallakin Kamfanin Mai na Kasa (NNPC).
Direbobin dai sun koka da cewa akasarin manyan hanyoyin kasar nan sun zama tarkon mutuwa inda mambobinsu ke rasa rayukansu a kullum.
“Kungiyarmu ta kasa gano wani kwakkwaran dalilin da ya hana gwamnati duba bukatunmu da nufin magance su,” inji sanarwar.