✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin iya karanta Littafin Risala ya hana wadansu zama alkalai a Gombe

A ranar Talatar da ta gabata ce Babban Jojin Jihar Gombe Mai Shari’a Hakila Y. Heman ya rantsar da sababbin alkalai 19 na kotunan lardi…

A ranar Talatar da ta gabata ce Babban Jojin Jihar Gombe Mai Shari’a Hakila Y. Heman ya rantsar da sababbin alkalai 19 na kotunan lardi 7 da za su rika alkalanci a jihar.

Da yake rantsar da sababbin alkalan Mai Shari’a Hakila Y. Heman, ya ce wadansu da dama da suka nemi zama alkalan sun fuskanci kalubale a wajen jarrabawa da intabiyu saboda ba su iya karanta littafin Risala ba. “Wadansu da yawa da suka nemi zama alkalan a wajen jarrabawar Intabiyu sun fuskanci kalubale sosai domin ba su iya karanta sharhin Risala ba,” inji Babban Jojin.

Ya ce daukar sababbin alkalan da Hukumar Shari’a ta Jihar ta yi ya biyo bayan ajiye aiki da wadansu alkalai suka yi ne bayan cikar shekarunsu a aiki wadansu kuma suka samu karin girma zuwa gaba.

Babban Jojin, ya ce sababbin alkalan ma’aikatan kotuna ne da suka karanta shari’a da magatakardan kotuna da suka cancanta aka dauka bayan cikakkiyar tantancewar da aka gudanar a kansu.

 Ya taya su murnar zama alkalai, kuma ya hore su cewa su rika gudanar da shari’a cikin adalci kamar yadda ya kamata kuma su dogara da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da kundin laifuffuka da hukuncinsu na Final Kod.

Mai shari’a Hakila Heman, ya ce wadanda suka karanci ilimin shari’ar dokokin Musulunci su ci gaba da neman ilimin Alkur’ani Mai girma da Tufatul Hukkam da Sharhin Askari da Sharhin Risala da Badurul Zaujaini da hadisai. 

Y a ce su sani ilimin addini yana daga cikin abubuwan da ake la’akari da shi daga ofishin Kadi kan zamansu alkalan shari’a, sai ya hore su cewa a matsayinsu na masu ilimi da suka samu horo a bangaren shari’a yana da kyau su zama masu daukar bayanan masu kara da kansu don hakan ne zai ba su damar gudanar da kotunansu yadda ya kamata.

Sannan ya ce su tabbatar suna rubuta rahotonsu na kowane karshen wata uku-uku kan kararrakin da suka yanke hukunci don bai wa hukumar kula da alkalan damar gudanar da aikinta na gane wanda yake da kwazo a tsakaninsu.