✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin hakuri ke haifar da yawan hadari a kan hanyoyi – Darakta

Daraktan Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa ta Jihar Bauchi (b.I.O) Injiniya Muhammed Benni Abdulkadir ya shawarci direbobin jihar su zamo masu bin doka da…

Daraktan Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa ta Jihar Bauchi (b.I.O) Injiniya Muhammed Benni Abdulkadir ya shawarci direbobin jihar su zamo masu bin doka da oda a lokacin da suke tuki a kan hanyoyin jihar Bauchi, inda ya ce hukumar ta fito da sababbin dabaru na hukunta duk wanda aka kama yana wasa da rayuwar jama’a a kan hanyoyin jihar.
Injiniya Muhammed Benni ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa a ranar Alhamis din makon jiya, inda ya ce rashin hakuri daga masu tuka ababen hawa ne yake haifar da yawan hadari a hanyoyin kasar nan, saboda kusan kowane direba yana sauri.
“Kuma yanzu hukumarmu ta fito da wasu sababbin dabaru na kama direbobi masu amfani da miyagun kwayoyi a lokacin da suke tuki, kuma muna kira ga direbobi marasa lafiyar ido su daina toka motoci da kansu domin yanzu duk wanda muka kama yana wasa da rayuwar jama’a, tabbas za mu gurfanar da shi a gaban kotu, don yi masa hukuncin da ya dace,” inji shi.
Alhaji Benni ya ce da ana tilsata direbobi su biya diyya yadda ya kamata, tabbas zai yi wahala a samu direban da zai yi wasa da rayuwar jama’a, kuma rashin hakan ne ya sa kadan ne daga cikinsu suke bin dokokin hanya a jihar.
“Sama da kashi 65 cikin 100 na direbobi maza ne ke haddasa haddura a kan hanyoyin kasar nan, duk dokar da aka kafa game da tuki mata sun fi kiyayewa fiye da maza,” inji shi.
Ya bukaci fasinoji cewa idan suka ga direba yana karya dokokin hanya musamman mugun gudu su taka masa birki.
Ya ce an samu raguwar haddura a farkon wannan shekara a jihar sakamakon yadda hukumar take wayar da kan direbobi ta kafafen watsa labarai, kuma ya bukaci wadanda lasisin tukinsu ya kare aiki su yi maza su sabunta tun kafin su shiga hannun hukumar.