Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce duk wani rikici da ake fuskanta cikin kasar nan a yanzu na faruwa ne a sakamakon rashin samun masu fada wa gwamnati gaskiya kan abin da ya kamace ta.
Farfesa Osinbajo ya ce galibin manyan kasar nan ba sa fitowa su fada wa gwamnati gaskiya da ba ta shawara kan ababen da za su kawo wa kasar ci gaba.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasar ya yi wannan furuci a wani taron tattaunawa na ’yan takarar jam’iyyar APC manema kujerar gwamnan jihar Anambra wanda uwar jam’iyyar ta shirya.
A yayin da yake jan hankalin dukkan masu ruwa da tsaki wajen fadar gaskiya da bayar da gudunmuwar da ta dace wajen ciyar da kasar gaba, Osinbajo ya kuma ce Najeriya ba za ta so ta fada yakin basasa ba.
A cewarsa, wajibi ne ’yan siyasa su kara himma wajen fadin gaskiya da kuma daukar matakan da suka dace wajen ganin an kawo karshen matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar.
Ya shawarci shugabanni da su mike tsaye su yi aikin da ya dace domin fidda kasar nan da kuma al’ummarta zuwa ga ci.
Kazalika, ya nemi masu fada a ji da manyan kasar a kan su yi tsayuwar daka wajen kiran mutane a kan gaskiya tare da gargadinsu a kan ababen da ka iya janyo rabuwar kai a kasar nan.