Wani matashi mai kimanin shekaru 23 a duniya, Michael Ogunbade wanda aka cafke bisa zargin aikata fashi da makami ya ce ya shiga harkar ne saboda rashin aikin yi.
Wanda ake zargin dai na daga cikin mutum 27 da jami’an tsaro suka kama sakamakon wani samame da suka kai maboyar bata-garin daban-daban a birnin Legas.
- Za mu shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da Malamai — Ganduje
- Yadda aka sace matan aure bayan kashe ’ya’yansu a Kaduna
Hakan dai ya biyo bayan korafin da masu ababen hawa suka yi na yi musu kwace suna tsaka da tuki a kan hanya.
Ya shaidawa ’yan jarida a shalkwatar ’yan sanda dake Ikeja cewa duk yunkurin sa na neman aiki a baya ya ci tura.
Ya ce, “A kokarina na kaucewa yunwa, na bi sahun sauran bata-gari a Abule-Egba wajen kwacen kudi daga hannun ’yan kasuwa.”
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta jihar, Muyiwa Adejobi ya ce sun kuma kama karin wasu mutane 27 bayan samun korafe-korafe daga wadanda lamarin ya ritsa da su, musamman a yankunan Ikeja da Agege da kuma Alimosho na jihar ta Legas.