✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin aiki ya ƙaru zuwa kashi 4.3 a Najeriya — NBS

Rahoton ya nuna yadda rashin aikin ya ƙaru idan aka kwatanta da shekarar 2023.

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta ce rashin aikin yi a Najeriya ya ƙaru zuwa 4.3 cikin kashi na biyu na shekarar 2024.

Rashin aikin yi a tsakanin matasa ya ragu daga 8.4 cikin kashin farko zuwa 6.5 a kashi na biyu na 2024.

Rashin aikin yi a tsakanin maza ya kasance kashi 3.4 yayin da na mata ya fi yawa da kashi 5.1.

A birane, rashin aikin yi ya kai kashi 5.2, yayin da a karkara ya kasance kashi 2.8.

“Adadin ma’aikatan da ke cikin jama’ar da suka kai shekarun aiki ya kasance kashi 76.1 cikin kashi na biyu na 2024,” in ji NBS,.

Adadin ya nuna yadda aka samu ƙarin kaso 73.1 a kashin farko na 2024.

Duk da haka, wannan adadin ya ragu idan aka kwatanta da kaso 77.1 da aka samu a kashi na biyu na 2023.

Hakazalika, adadin ’yan Najeriya da ke aiki ya ragu zuwa 9.2 a kashi na biyu na shekarar 2024, idan aka kwatanta da kashi 10.6 a kashin farko na wannan shekara.

Adadin ya kasance kashi 7.1 ga maza, yayin da mata suka kai kashi 11.2.

Rahoton ya bayyana cewa adadin waɗanda ke aiki ba a ƙarƙashin hukuna ba ya fi yawa da kashi 93, yayin da kashi 3.7 na mutanen da suka kai shekarun aiki ke yin noma don samun abinci.