Rasha ta kulla wata yarjejeniyar bai wa gwamnatin Taliban a Afghanista man fetur da dizel da kuma alkama na tsawon shekara guda.
A karkashin yarjejeniyar, Rasha za ta ba gwamnatin Taliban kimanin tan miliyan daya na man fetur da man dizel da kuma ton miliyan daya na alkama a duk shekara.
- Gwamnatin Amurka da ta Taliban sun yi musayar fursunoni
- Taliban za ta soma sayen makamashi daga Rasha
An sa hannu kan yarjejeniyar ne bayan da wani kwamitin kwararru na ’yan Afgahanistan su ka yi makwanni suna tattaunawa da jami’an gwamnatin Rasha a Moscow.
’Yan kwamitin sun kuma zauna a can har sai da Minista Azizi ya kai ziyara a watan Yuli.
Mukaddashin Ministan Ciniki da Masana’antu na gwamnatin Taliban, Haji Nooruddin Azizi ne bayyana haka a hirarsa da Reuters ranar Talata.
Yarjejeniyar ta wucin gadi ce, a matsayin gwaji, ana kuma sa ran ta yi aiki kafin bangrorin biyu su sake sa hannu kan wata yarjejeniyar ta tsawon lokaci a nan gaba.
Wannan yarjejeniya ita ce ta farko ta fuskar tattalin arziki da Afghanistan ta kulla da wata kasa tun lokacin da Taliban ta kwace mulki a kasar a shekarar 2021.
Rasha ba ta amince da Gwamantin Taliban ba a hukumance, amma ta karbi bakuncin shugabanin Taliban a kasarta na wani lokaci kafin su kwace gwamnati.
Sannan kuma, Ofishin Jakadancin Rasha na daga cikin ’yan kadan da ba su rufe ba a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.