Hamshakin attajirin duniya kuma mamallakin kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya ce a shirye yake ya gana da gwamnatin Taliban muddin hakan zai taimaka wajen kawar da cutar shan-inna a kasar Afghanistan.
Bill Gates ya fada wa jaridar Telegraph a ranar Litinin cewa, zai yi bakin kokarinsa wajen tallafa wa yaki da shan-inna a kasar ta hannun Gidauniyarsu ta ‘Bill and Melinda Gates’.
- Qatar za ta karbi bakuncin Gasar Kofin Asiya ta 2023
- Jirage marasa matukan Rasha sun yi wa Ukraine ruwan bama-bamai
- NAJERIYA A YAU: Yajin Aikin ASUU: Nasara Ko Asara?
Ya ce tuni abokan huldar gidauniyarsu suka gana da Taliban a Qatar, tare da nuna jin dadinsa kan yadda kasar ta kyale ministan lafiyarta saboda a cewarsa, yana da sanin makamar aiki.
Gates ya nuna damuwarsa kan yadda shugabannin duniya ba su ba da muhimmanci yadda ya kamata ba wajen yaki da wannan cuta ta shan-inna.
Cutar shan-inna, cuta ce mai hadarin gaske wadda ka iya shanye sassan jiki cikin kankanin lokaci idan an kamu da ita, musamman ma a tsakanin kananan yara.
A halin da ake ciki, cutar na ci gaba da addabar kasashen Afghanistan da Pakistan, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana.