Wata cuta da ba a san irinta ba ta yi sandiyar mutuwar yara 20 a yankin Baghran na kasar Afghanistan.
Daraktan Yada Labarai da Al’adu na Kudancin Lardin Hemand, Hafiz Rashid ya bayyana a ranar Laraba cewa yaran da abin ya shafa sun rasu ne a cikin kwana biyu.
- An kama matashi ya saci satar giyar N200,000
- Matashi zai yi wata 3 a kurkuku kan satar wayar N30,000
“Muna zargin shan gurbataccen ruwa ne ya haddasa barkewar annobar”, in ji shi.
Yanzu haka dai sauran wadanda suka kamu da cutar suna kwance a asibitocin sha-ka-tafi suna karbar magani.
Rashin ababen more kamar cibiyoyin lafiya da tsaftataccen ruwan sha na barazana ga rayuwar mutane da dama da suka kamu da cututtuka da za a iya magancewa a yankunan karkara da wurare masu nisa.