Tsohon Shugaban Kasar Guinea, Moussa Dadis Camara ya musanta zargin kisan kiyashin da kotu take masa a zamanin mulkinsa.
Ana zargin Moussa ne tare da wasu tsofaffin jami’an gwamnatinsa 10 da laifin kisan mutane 156 da yi wa mata 109 fyade a wata zanga-zanga a watan Satumbar 2009, a filin wasa na Conakry da ke kasar.
- Shugaban Afirka ta Kudu ya kubuta daga yunkurin tsige shi
- Majalisa ta ba NNPC mako daya ya kawo karshen wahalar mai a Najeriya
Ana kuma zargin su da laifukan cin zarafi da tada hankali da satar mutane da kuma fashi.
Alkalin kotun, Ibrahima Sory Tounkara, ya ce Moussa ya musanta zargin, tare da shan alwashin barin kasar har abada idan kotu ta same shi da laifi.
Sai dai lauyan tsohon dogarin Moussa, Aboubacar Sidiki Diakite da aka fi sani da Toumba, ya zargi tsohon shugaban da shirya kisan, da kuma rashin lafiyar karya.
Moussa Camara ya mayar da martani da cewa Toumban ne ya hana shi zuwa filin wasan don hana rikicin, kuma a lokacin Toumba na dauke da gurneti a jikinsa da suka tilasta shi ya kyale shi a lokacin.
A shekarar 2008 ce Kyaftin Camara ya kwace mulkin kasar Guinea bayan rasuwar tsohon Shugaban Kasar, Lansana Conte, wanda ya jagoranci kasar na tsawon shekara 24 tun bayan ’yanci.
A watan Disambar 2009 ne dai Toumba ya harbi Camara a ka da bindiga, wanda ya sanya ya tsere zuwa kasar Maroko domin neman lafiya, kafin daga bisani ya koma Burkina Faso.
A watan Yulin 2015 ne mahukuntan Guinea suka gurfanar da shi a gaban kotu, bisa zargin kisan kiyashin da aka yi a filin wasan, da karin wasu laifukan.