Sojoji sun sake kama tsohon shugaban gwamnatin sojin Guinea Moussa Dadis Camara, bayan ya tsere daga gidan yari da ke Conakry, babban birnin kasar Guinea.
A wata sanarwa da ya fitar, babban hafsan sojojin gwamnatin rikon kasar Guinea, Janar Ibrahima Sory Bangoura, ya bayyana cewa Moussa Dadis Camara na cikin koshin lafiya kuma yanzu haka ya koma babban gidan yarin da ke birnin Conakry.
Ya kara da cewa an kama Kanar Moussa Tiegboro Camara da kuma Kanar Blaise Gomou, da tsere tare da Camara a safiyar Asabar, an kuma mayar da su gidan yari kuma ana yin duk abin da ya kamata domin ragowar mutum na karshe da ya tsere, wato Claude Pivi.
Blaise Gomou shi ne ministan yaki da ta’addacnci a gwamnatin Camara, Claude Pivi kuma ministan tsaron shugaban kasa.
Ma’aikatar shari’ar kasar ta sanar cewa Ofishin Antoni-Janar ya ba da umarnin fara shari’a kan manyan laifuka da kae zargin Camara da mukarraban nasa.
A shekarar 2008 ne Moussa Dadis Camara ya yi juyin mulki, zuwa 2010 da aka kifar da shi kuma ya tafi gudun hijira a kasashen waje.
A watan Disambar 2021 ya koma Guinea inda daga baya kuma aka zarge shi da mutuwar mutane 150 da jikkata wasu sama da 1,000 a yayin murkushe zanga-zangar da aka yi a Conakry a lokacin mulkinsa a watan Satumbar 2009.
Moussa Dadis Camara, tare da wasu jami’an soji guda biyu, an tsare su a gidan yari da ke yankin Kaloum.