Wasu sojoji dauke da muggan makamai da fuskansu a rufe sun kai hari kusa da fadar shugaban kasar Guinea, inda suka sace tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Moussa Dadis Camara daga gidan yari.
Wata majiyar tsaro ta ce sojojin sun shiga gidan yarin ne da karfin tsiya da misalin karfe 4 na asuba, inda suka bayyana bayyana cewa “sun zo ne su ’yanta Kyaftin Dadis Camara”.
- Zaɓen Kano: Ranar Litinin Kotun Daukaka Kara Za Ta Saurari Karar Abba
- Yadda maza suke sakar wa mata daukar nauyin gida
Luguden wuta sun razana mazauna kasar da ke karkashin mulkin soji, inda ake tsare da kyatin Camar da jami’an gwamnatinsa a Conakry, babban birnin kasar.
Mazauna sun ce tun da aka fara harbe-harben, an hana girke motocin yaki tare da hana shiga da fita daga Kaloum, yankin da fadar shugaban kasar da hedikwatar tsaro da ofisoshin gwamnatin kasar da ma gidan yarin suke.
Wani ma’aikacin kotu ya ce da shigar maharan suka zarce kai-tsaye zuwa inda yake, suka dauke shi tare da wasu fursunoni , zuwa wani wuri da har yanzu ba a gano ba.
Ya bayyana cewa sun kuma tafi da akalla mutum biyu daga cikin jami’an tsohuwar gwamnatin Dadis Camara daga gidan yarin da ake tsare da su kan zargin kisan kiyashi a zamanin mulkinsa a 2009.
Kafofin yada labaran kasar sun bayyana cewa an yi awon gaba da Dadis Camara tare da Moussa Tiegboro Camara da kuma Claude Pivi a harin ne aka kai babban gidan yarin.
Lauyan Camara, Jocamey Haba ya bayyana cewa, “Antoni Janar ya tabbatar mini cewa wasu mahara dauke da manyan makamai sun yi awaon gaba da wanda nake karewa daga gidan yari.”
Da yake tsokaci kan shari’ar Kyaftin Camara da ke tafe, lauyan ya ce, “Ina tunanin garkuwa da shi aka yi, domin yana da kwarin gwiwa game da adalcin bangaren shari’ar kasar nan, shi ya sa ba zai taba yin wani yunkuri na tsewera.
“Ya kara da cewa, rayuwar wanda yake karewan yana “cikin hadari”.
Wata majiya a filin jirgi ta ce babu jirgin da ya tashi daga babban filin jirgi na Conakry saboda ma’aikata sun kasa zuwa filin jirgin daga inda suka kwana a Kaloum.
A watan Satumban 2021 ne sojoji karkashin jagoranci Kanar Mamady Doumbouya suka yi kifar da gwamnatin shugaba Alpha Conde a kasar mai yawan al’umma miliyan 14, kuma tun daga lokacin sojoji ke mulkin kasar.
Kafofin yada labaran kasar dai sun bayyana cewa abin da ya faru ranar Asabar ba juyin mulki ba ne.