Sojojin Rasha da sun yi awon gaba da wani Dakarta-Janar da ke aiki a masana’antar nukiliyarta ta Zaporizhzhia.
Gwamnatin Ukraine na zargin dakarun Rasha da azabtarwa da kuma wulakanta babban jam’in a masana’natar nukiliyar da ke yakin Kudancin Ukraine da ke karkashin ikon sojojin Rasha.
- An kama mutum 3 da suka yi yunkurin sace ubangidansu
- Bollywood: Kalubalen da fina-finan Indiya ke fuskanta
“Sojojin Rasha sun yi gakuwa da Mataimakin Darakta-Janar na Sashen Kula da Ma’aikta a Masana’antar Nukiliya ta Zaporizhzhia, Valeriy Martyniuk,” in ji sanarwar da gwamnatin Ukraine ta fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta yi kira ga Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi da zai kai ziyara Rasha da ya sa baki Rasha ta sako jami’in.