Rasha ta shiga sahun jerin kasashen da ke neman samun izinin karbar bakuncin gasar kofin nahiyar Turai a shekarun 2028 da kuma 2032.
Duk da dakatarwar da aka yi mata biyo bayan mamayar da ta yi wa Ukraine, hakan bai hana ta shiga sahun wadanda ke son karbar bakuncin gasar ba.
- Shugabancin APC na Kasa: Shinkafi ya janye wa Abdullahi Adamu
- Majalisa ta bukaci CBN ya tilasta amfani da kudaden tsaba
A ranar Laraban ne Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiryar Turai (UEFA), ta bayyana sunayen kasashen da suka nuna sha’awarsu ra karbar bakuncin gasar, wadanda suka hadar da Rasha da Turkiyya da Ingila da kuma Ireland, a matsayin wadanda za su yu yi gogayya wajen neman karbar bakuncin gasar ta 2028.
A watan Satumba ne ake sa ran UEFA za ta sanar da kasar da za a gudanar da gasar.
Rasha dai ita ce ta karbi bakuncin kofin duniya da aka yi a 2018.
Sai dai an dakatar da gudanar da wasan karshe na wasan zakarun nahiyar turai (Champions League) na wannan shekarar da za a gudanar a kasar, sakamakon yakin da kasar ta kaddamar a kan Ukraine.
Turkiyya na sa ran karbar bakuncin gasar bayan da ta yi rashin nasara a wajen Jamus wacce a yanzu zata amsa bakuncin gasar na shekarar 2024.