Jiragen sojin kasar Rasha sun kashe mayakan kungiyar IS akalla 11 a yankin Gabashin kasar Syria.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syrian Observatory da ke sanya ido kan kashe-kashen da ake yi a rikicin Syria, ta ce jiragen sun kai harin ne a tsakanin yankunan Palmyra da Al-Sukhna a ranar Alhamis.
- NATO ta yi zaman sasanci kan rikicin Ukraine da Rasha
- Fitattun mutanen da suka shiga tsaka mai wuya kan karya dokar COVID-19
“Mayakan jihadin na buya ne a cikin koguna a yankin,” inji shugaban kungiyar, Rami Abdel Rahman.
Ya ce baya ga mayakan kungiyar IS 11 da jiragen suka kashe, wasu 20 kuma sun samu raunuka a hare-haren.
Rami Abdel Rahman ya ce jiragen Rasha sun kai hare-haren akalla 229 a bara a yankin da a halin yanzu mazaunansu suka kaurace masa.
Ya bayyana cewa harin na ranar Alhamis shi ne mafi muni da jiragen Rasha suka kai tun daga watan Nuwamba zuwa yanzu.
A watan Nuwamban 2021 ne jiragen Rasha suka hallaka mayakan IS 16 a wani hare-haren da suka kai.
A baya dai, kungiyar IS ta mamaye yankunan da ke tsakanin Syria da kasar Iraqi, wadanda kungiyar ta ayyana a matsayin daularta.
Amma daga baya dakarun gwamnatin Iraqi da Syria da ke samun goyon bayan Amurka da Rasha da sauran kasashe suka fatattake su a watan Maris na 2019.
Daga bisani kuma akasarin mayakan kungiyar suka koma maboyarsa da suka bari, suna kai wa dakarun gwamnati da kawayensu hari.