Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya rattaba hannu kan wata doka da ke ba shi damar sake tsayawa takara karo biyu bayan cikar wa’adinsa na yanzu a shekarar 2024.
Sabowar dokar, ta wa Mista Putin damar ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2036 idan ya zabi yin hakan ya kuma sake cin zabe.
- ‘Za mu fasa shagunan ’yan kasuwar da ke boye kayan masarufi a Kano’
- Damfara ta miliyan N450 aka yi rana guda —Ummi Zee-Zee
- Caca: Yadda N50 ta yi sanadiyyar kisan mutum 3
- An tsare tsoffin hafsoshin soji saboda sukar gwamnatin Turkiyya
Putin ya halarci bikin sanya hannun kan yarjejeniyar sabuwar dokar da aka gudanar ta bidiyo, wanda kungiyoyin kwadago, kamfanoni da kuma jami’an gwamnati kasar suka halarta a gidan gwamnati da ke Novo-Ogaryovo a ranar 31 ga Maris, 2021.
Fadar Shugaban Kasar Rasha ta Kremlin ta bayyana hakan ne ta wani sako da aka wallafa a shafin intanet na gwamnatin kasar a ranar Litinin.
Wannan wani bangare ne gagarumin sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin da aka faro a shekarar da ta gabata.