✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rarara zai ba da kyautar mota da babur

Wanda ya lashe gasar rawar zai samu kyautar galleliyar mota

Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarawa ya sa gasar rawa ta wakar Dogara ya dawo, wadda ya rera wa tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da ya dawo jam’iyyar APC daga PDP.

Da yake bayanin yadda gasar za ta kasancewa, daraktan bidiyon wakar, Ali Nuhu ya bayyana cewa duk wanda yake son shiga gasar, zai sauke wakar Dogara ya dawo daga shafin YouTube mai suna Dauda Kahutu Rarara ko a shafin Maishadda Global Resources, sai a yi bidiyon rawar da ake ganin za ta yi kyau da wakar.

Rarara a lokacin daukan bidiyon wakar Dogara ya dawo. (Hoto: Ali Nuhu)

Idan aka dauki bidiyon rawar da aka yi, sai a tura a shafin Instagram, sannan a ambaci sunan Abubakar Bashir Maishadda wanda shi ne furodusan wakar @realabmaishadda da Mataimakan Daraktan wakar; Sheikh Isa Aloli @sheik_isa_aloli; da Nasiru Ali Koki @nasiralikoki da Aminu S. Bono @aminusbono; sannan a ambaci #Dogarayadawochallenge.

Wanda ya lashe gasar zai samu kyautar mota, na biyu zai samu babur mai kafa uku, na uku kuma zai samu babur, sannan daga na hudu zuwa na 10 kowa zai samu kyautar Naira dubu 150.