✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rarara ya nemi kotu ta yi watsi zargin taurin bashin N10m da ake masa

Ana dai tuhumarsa ne da taurin bashin Naira miliyan 10

Fitaccen mawakin siyasar nan da ke Jihar Kano, Dauda Adamu Kahutu (Rarara) ya bukaci Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ta yi watsi da karar da aka shigar da shi a gabanta.

Wani dan kasuwa, Muhammad Ma’aji ne dai ya maka mawakin a gaban kotun bisa zarginsa da taurin bashin kudi har Naira miliyan 10 da ya sayi wayoyin salula ya raba kyauta amma ya ki biya.

Sai dai a zaman kotun, wacce ke unguwar Rijiyar Zaki ranar Talata, karkashin jagorancin Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, lauyan Rarara, G.A. Badawi, ya shaida wa kotun cewa tuhumar ba ta da tushe, don haka ya bukaci a yi watsi da ita.

Ya ce sun mika bayanansu ga kotun da kuma mai kara, amma mai shigar da kara ya tsaya kai da fata cewa an yi hakan a makare.

Mai karar dai ya ce yana da rubutattun hujjojin da ke dauke da bayanan duk cinikin da ya yi da mawakin tun 2021, amma ko sisi bai ba shi ba.

Daga nan ne alkalin ya bukaci lauyan masu shigar da kara da ya ba lauyan masu ba da kariya amsa a rubuce da ma ita kanta kotun.

Kazalika, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 12 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron karar.