✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rarara ya ba Shagiri Girbau kyautar babur

Fitaccen mawakin Jam’iyyar APC da Shugaba Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya gwangwanje dan wasan barkwanci Shagiri Girbau na Kano da kyautar sabon babur, bayan da…

Fitaccen mawakin Jam’iyyar APC da Shugaba Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya gwangwanje dan wasan barkwanci Shagiri Girbau na Kano da kyautar sabon babur, bayan da aka ce Girbau ya koma APC.

A wani faifan bidiyo da hotuna da Aminiya ta gani, an nuna lokacin da Rarara yake mika wa Shagiri Girbau mabudin babur din, sannan shi kuma yake masa godiya. An nuna wani faifan bidiyo da aka nuna Shagiri Gurbau tare da Gwamna Ganduje, kuma aka ji muryar Shagiri a ciki yana cewa ya gane gaskiya.