Sanannen abu ne cewa yadda halitta da dabi’ar mata ta bambamta da ta maza, haka ma tsarin tarbiyantar da su domin zamowa mutane na gari, ba daya yake ba.
Baya ga haka, tun daga tasowarsu, suke fara kwaikwayon abubuwan da ake aiwatarwa a inda suke, lokacin da suke wasa, ko kuma don abin da suke gani ana yi yau da gobe.
- Yadda jinin al’ada ke hana ni zuwa makaranta —Daliba
- Ranar Yara Mata: A Najeriya aka koyar da mu kamar ’ya’yan turawa —A’isha Isma’il
- NAJERIYA A YAU: “Ban So Ba Aka Yi Min Aure A Shekara 14 “
Kasancewar wannan mataki ne da kowa kan taka kafin ya zama babba, mun tattauna da wasu iyaye a Arewacin Najeriya, don jin bambamcin da ake samu tsakanin rainon da namiji da kuma ’ya mace.
Hajiya Aishatu Isma’il, wacce tsohuwar ministar ce a Najeriya, ta ce mata sun fi fitina a lokacin da suke kanana, sai dai da zarar mazan sun kai shekaru 11 ko 12 sai su zarta su.
Ta ce duk da cewa iyaye da dama sun fi shakuwa da ’ya’yansu maza kafin su kai wannan matakin, shakuwar na komawa kan ’ya’yansu mata da zarar sun fara girma.
“Kuma da sun fara tasawa, kasancewar maza ba sa zama a gida, sun fi jefa ki a fargaba, saboda tunanin me za a zo a ce miki sun yi.
“Su kuwa mata kin ga ai sun fi zama a gida a wadannan shekarun.
“Amma fa dukkansu tarbiyarsu da wahala”, in ji ta.
Mata sun fi saukin kai
Ita ma Hajiya Hajara Auwal, wadda ma’aikaciya ce a Jihar Kano, ta ce tarbiyar ’ya mace ta fi ta namiji sauki a lokacin da suke tasowa, musamman kasancewar sun fi saukin kai, da wasanninsu cikin gida inda za a ga duk abin da suke yi.
“Amma kin ga namiji, ko wasan ba ya kaunar ya yi a cikin gida. Idan ma ya yarda ya yi a gidan ba zai yi na kwanciyar hankali ba.
“Ko da abokansu suka hadu idan ki ka lura za ki ga tun ba su fi shekaru uku ba sun iya kokawa da fadace-fadace da kwallon kafa.
“Mata kuma kin ga yawanci wasansu bai wuce na ’yar tsana ko ayyukan gida ko raino ko makamantansu ba.
“Kuma yawanci a kusa da ke ma suke yi suna kokarin ki taya ta wasansu.”
’Ya’ya maza sun fi biyayya
Ita ma Hajiya Zulaihat Muhammad da ke koyarwa a Kano, ta ce idan suka fara tasawa, ’ya’ya maza sun fi mata biyayya ga malamai.
“Mace za ki ga wani lokacin sai kin hada da bulala da barazana tukun, amma namiji kina nuna baki ji dadi ba, zai daina.
“Kin ga ni bayan kasancewata uwar maza da mata kuma malamar makaranta ce da na koyar a makarantun maza da mata, don haka na fuskanci abubuwa da dama daga bangarorin biyu,” kamar yadda ta bayyana.
Zulaiha ta ce baya ga haka, kulawar da ake bai wa mace idan ta kaimatakin budurci ta ninka wacce ake bai wa mazan.
Ta bayyana cewa hakan ke kara alamta wahalar da rainon ’ya macen ke da ita.