Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gabatar da jawabinsa a ranar Talata ga taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a birnin New York na Amurka.
Ranar dai ita ce za ta zama ya farko a taron na bana, kuma wannan shi ne karo na farko da zai halarci taron a matsayin Shugaban Najeriya.
- Allah Ya yi wa Ciroman Dukku rasuwa a Gombe
- Gwamnatin Obasanjo ta fi kowacce bunkasa tattalin arzikin Najeriya — El-Rufai
Kakakin shugaban, Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Asabar.
Ya ce ana sa ran shugaban zai bar Abuja zuwa birnin na New York ranar Lahadi, kwana daya bayan dawowarsa daga taron G-20 a kasar Indiya.
Yayin tafiyar dai, Tinubu zai samu rakiyar Gwamnoni Umo Eno (Akwa Ibom); Mohammed Inuwa Yahaya (Gombe State); Hope Uzodinma (Imo); Uba Sani (Kaduna); AbdulRahman AbdulRazak (Kwara) da kuma Seyi Makinde (Oyo).
Kazalika, shugaban zai samu rakiyar Shugaban ma’aikatan fadarsa, Femi Gbajabiamila da ministocinsa, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar (Harkokin Waje); Wale Edun (Kudi da Tattalin Arziki); Dr Mohammed Pate (Lafiya); Abubakar Badaru (Tsaro); sai Dele Alake (Ma’adinai).
Kazalika, a cikin ’yan tawagar akwai Ministar Walwala da Yaki da Talauci, Dr Betta Edu da na Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari, Dr Doris Uzoka-Anite.
Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da kuma Shugabar Hukumar da ke kula da ’yan Najeriyar da ke kasashen waje (NIDCOM) Abike Dabiri-Erewa da sauran kusoshin gwamnati za su kasance a cikin tawagar.