✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa Ciroman Dukku rasuwa a Gombe

Ya rasu yana da shekara 53 a doron kasa.

A wannan Asabar din Allah Ya karbi rayuwar Ciroman Dukku, Injiniya Yakubu Abdulkadir Rasheed, bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar jinya yana da shekara 53 a doron kasa.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na ya jajanta wa Masarautar Dukku bisa wannan rashi wanda aka gabatar da jana’izarsa a Fadar Mai Martaba Sarkin Gombe da Yammacin wannan rana.

A sakon ta’aziya da Gwamnan ya fitar ta bakin Babban Daraktan Yada Labaran Gidan Gwamnatin Jihar Isma’ila Uba Misilli, ya ce rasuwar Ciroman Dukku gibi ne mai wuyar cikewa.

A cewar sakon, marigayin ya ba da gudunmawa sosai kafin rasuwarsa musamman a lokacin da ya yi aiki a matsayin Shugaban Hukumar Ruwa ta Jihar Gombe.