✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cibiyar Binciken Aikin Gona ta soma bikin cika shekara 100 da dashen itatuwa

Itatuwan da aka samar suna da matukar amfani ga Dan Adam domin hana zaizayar kasa.

Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta fara bikin cika shekara 100 da kafuwarta da bikin dashen itatuwa.

Da yake jawabi a wajen bikin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabiru Bala ya bayyana cewa dashen itatuwan shi ne mafi muhimmanci da tarihi ba zai manta da shi ba.

Ya ce itatuwan da aka samar suna da matukar amfani ga Dan Adam da kuma hana zaizayar kasa.

Farfesa Kabiru Bala ya ce a cikin shekara 100 da cibiyar ta yi ta gudanar da bincike masu yawa wadda ya ba manoma damar cin moriyar binciken.

Shugaban Jami’ar ya bukaci masu ruwa da tsaki a fannin noma da su shiga a dama da su ta hanyar daukar nauyin fadakar da mutane irin sabbin dabarun noma da cibiyar ta samar.

A cewarsa, ta haka ne manoma za su ci gajiyar binciken da aka samar a zamanance.

Ya kuma shawarci ma’aikata da daukacin al’umma da su dasa akalla tushe biyar na itatuwa mabambanta.

Shi ma da yake jawabi, Babban Daraktar Cibiyar Binkiken Aikin Gona (IAR), Farfesa Muhammad Faguji Ishiyaku ya ce an yi dashen itatuwan ne bisa la’akari da muhimmanci da itatuwa ke da shi ga rayuwar al’umma da kuma kare muhalli.

Faguji Ishiyaku ya ce sun samar da itatuwa daban-daban domin dashen da kuma rabawa ga daukacin ma’aikata da ke cibiyar.

Ya ce sun samar da Tsamiya da Kadanya da Gwanda da Mangwaro da kuma itacen Karo da sauransu.