Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) ta sanya Litinin 24 ga watan Oktoba da muke ciki a matsayin ranar da dalibanta za su dawo domin ci gaba da karatu.
Jami’ar ta fito da sanarwar ce a ranar Laraba, bayan janye yajin aikin kungiyar malamain jami’o’i (ASUU) da sukayi na tsawon wata takwas.
- Cough: Sabuwar wakar Kizz Daniel ta yi zarra
- Karin haraji zai rage basukan da ake bin Najeriya —Minista
Daraktan Hulda da Jama’a na ABU, Auwalu Umar, a cikin wata sanarwa, ranar Laraba, ya ce Majalisar Jami’ar ce ta sanar da haka bayan zaman gaggawa da ta yi bayan janye yajin aikin kungiyar ASUU.
Majalisar Jami’ar, a zamanta na 516, ta amince da ranar dawowar da kuma sabunta jadawalin karatu na shekarar 2021/2022.
Ya ce, sabunta jadawalin karatun ya zama wajibi kasancewar wanda aka tsara a baya 25 bai yi aiki ba saboda yajin aikin ASUU.