✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Litinin NFF za ta gabatar da Le Guen a matsayin sabon kocin Super Eagles

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta zabi tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Faransa, Paul Le Guen a matsayin sabon mai…

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta zabi tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Faransa, Paul Le Guen a matsayin sabon mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, inda ta ce za ta gabatar da shi a ranar Litinin mai zuwa domin ba shi damar ci gaba da hora da ’yan wasan ta Super Eagles.
Paul Le Guen yana daya daga cikin wadanda suka nuna sha’awar zama masu horar da kungiyar tare da mai rikon kungiyar Salisu Yusuf da kuma Tom Saintfiet,
Le Guen kafin ya koma horar da ’yan wasan tsohon dan wasan kwallon kafa ne da ya buga wa kasar Faransa wasa sau 17, sannan ciwo ya hana shi zuwa gasar cin Kofin Duniya a 1994.
Paul Le Guen ya yi murabus da buga wasan kasa da kasa bayan wani wasan sada zumunta a 1998.
Mai shekara 52, Paul Le Guen ya samu nasara sosai a harkar horarwa musamman lokacin da ya horar da kungiyar kwallon kafa ta Olympic Lyon suka lashe gasar rukunin na daya na kasar Faransa (League 1) sau uku a jere.
Kuma Le Guen ya horar da Stade Rennais da Paris Saint-Germain da Glasgow Rangers da kuma kasar Kamaru.
Sai dai Salisu Umar ya ce ba zai karbi matsayin mataimakin mai horar da ’yan wasan ba, wanda hakan ya sa Hukumar NFF ta ce tana sauraron duk mai bukatar zama mataimakin ya nuna sha’awarsa.
Wani ma’aikacin Hukumar NFF ya ce “Yanzu dai babu mataimaki ga Le Guen, don haka duk wanda yake bukata sai ya nuna, duk da cewa mun zabi Le Guen ne da nufin su yi aiki da Salisu Yusuf domin Salisu ya karu da shi sosai kuma ya kara koyon harkar horar da ’yan wasan saboda gaba, amma sai Salisu ya ki amincewa da hakan. Don haka hukumar take tunanin nemo wanda zai zama mataimakin Le Guen a madadinsa.”